Wasu sun kashe mutum 7 ’yan gida ɗaya a Kano
[ad_1]
Mazauna unguwar Dorayi Chiranchi da ke cikin birnin Kano, sun shiga tashin hankali bayan wasu da ba a san ko su wan ene ba suka shiga gidan wani magidanci mai suna Haruna Bashir, tare da kashe matarsa da ’ya’yansa shida.
Mazauna yankin sun ce lamarin shi abun tashin hankali mafi muni da suka taɓa gani.
Waɗanda abin ya shafa sun haɗa da matar gidan, Fatima Abubakar mai shekaru 35, da ’ya’yansu: Maimuna (17), Aisha (16), Bashir (13), Abubakar (10), Faruk (7), da Abdussalam wanda bai kai shekara biyu ba.
Rahotanni sun ce an kai musu hari ne da muggan makamai bayan ɓata-garin sun ɓalle gidan da ke Dorayi Gidan Kwari a ranar Asabar.
Wani mazaunin yankin, Kabiru Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya girgiza al’umma matuƙa.
“Har yanzu muna cikin kaɗuwa. Babu wanda zai iya bayyana dalilin da ya sa aka kashe iyalin mutum gaba ɗaya, ko kuma wane ne ya aikata hakan,” in ji shi.
Ibrahim ya ƙara da cewa an ɗauki gawarwakin mamatan zuwa Asibitin Ƙwararru na Murtala Mohammed, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayar da umarnin gudanar da bincike.
Ya ce sashen binciken manyan laifuka (CID) na rundunar ya riga ya fara bincike domin gano waɗanda suka aikata laifin.
“Rundunar tana miƙa sakon ta’aziyyarta ga iyalan mamatan da al’ummar Dorayi Chiranchi. Muna tabbatar wa jama’a cewa an fara bincike kuma za a yi adalci,” in ji Kiyawa.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link