AFCON 2025: Nijeriya Ta Kare A Matsayi Na Uku Bayan Doke Masar

[ad_1]

Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya da ke buga gasar cin kofin ƙasashen nahiyar Afirika a ƙasar Morocco ta samu nasarar samun kyautar tagulla bayan ya samu nasarar doke ƙasar Egypt a bugun Fenarati.

Bayan kammala mintuna 90 ba tare da wata ƙasa ta jefa ƙwallo a wasan na yammacin Asabar ba, alƙkalin wasa ya busa tashi, inda aka tafi zuwa bugun Fenarati kai tsaye ba tare da ƙarin mintuna 30 da aka saba yi a al’adance ba.

  • Sin Na Daga Cikin Manyan Abokan Cinikayya 3 Na Zimbabwe A Shekarar 2025
  • Ƴansanda Sun Cafke Mutum Biyu Da Ake Zargi Da Kisan Wata Lauya A Abuja

Dele Bashiru ya fara buga wa Nijeriya fenarati kuma ya ɓarar bayan mai tsaron ragar Egypt ya ture ƙwallon, daga ɓangaren Egypt Mohamed Salah da Omar Marmoush ne suka ɓarar.

Akor Adams, Alex Iwobi, Moses Simon da Ademola Lookman ne suka ci wa Nijeriya ƙwallaye 4 a bugun fenarati wanda ya yi sanadin samun nasarar ƙarewa a matsayi na 3 a gasar.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *