’Yan sanda sun ceto wanda aka sace da farautar maharan a Gombe

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta samu nasarar ceto wani mutum da aka sace a ƙauyen Tingile da ke yankin Birin Fulani a ƙaramar Hukumar Nafada.

Mutumin mai suna Alhaji Adamu Bappah mai shekara 48, an sace shi ne da safiyar Talata bayan wasu mutane ɗauke da makamai suka mamaye wurin kiwon shanunsa.

A cewar Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Buhari Abdullahi lamarin ya faru ne a ranar 11 ga Fabrairu, 2026, da misalin ƙarfe 3:00 na dare, lokacin da wasu da ba a san ko su wanene ba ɗauke da sanduna, adda da wuƙaƙe suka kai hari.

Ya ce, maharan sun ɗauki Alhaji Adamu Bappah da ɗansa kafin su yi awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba. Dan nasa ya samu raunuka, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likita.

DSP Abdullahi ya bayyana cewa rundunar ta ƙaddamar da aikin ceto cikin gaggawa tare da haɗin gwiwar jami’an ’yan sanda, mafarauta na gari da kuma ’yan banga.

“Wannan aiki ya kai ga ceto mutumin da misalin ƙarfe 3:00 na rana a dajin Dawo da ke ƙaramar Hukumar Kwami,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, an kai wanda aka ceto asibiti domin duba lafiyarsa kafin daga bisani a miƙa shi ga iyalansa.

Ya kuma tabbatar da cewa ana ci gaba da farautar waɗanda suka aikata wannan mummunan aiki domin kamo su.

Rundunar ta jaddada ƙudirinta na yaƙi da aikata laifuka tare da tabbatar da tsaro da zaman lafiya ga al’ummar Jihar Gombe.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *