Kamfanonin Sin Da Amurka Sun Fadada Hadin Gwiwa A Sabuwar Shekara
[ad_1]
An gudanar da bikin cika shekaru 20 da gudanar da shirin musayar hadin gwiwa a tsakanin kamfanonin kasar Sin da kasar Amurka wato CMP, a ranar 9 ga wata. An gudanar da bikin bisa hadin gwiwar kungiyar raya cinikayya ta kasar Sin, da ofishin jakadancin kasar Amurka dake kasar Sin da ma sauran hukumomin da abin ya shafa. A yayin bikin kuma, an yi gasar wasan kallon kwando da taron karawa juna sani, inda wakilai masu nasaba da harkokin masana’antu da kasuwanci na kasashen Sin da Amurka kimanin 250 suka halarta, tare da cimma sakamako masu gamsarwa.
Shugaban kungiyar bunkasa kasuwanci ta kasar Amurka dake kasar Sin Michael Hart ya bayyana cewa, a ko wace shekara, kungiyar ta na bincike kan yanayin kasuwanci a kasar Sin, domin kara sanin ra’ayoyin kamfanonin kasar Amurka dake kasar Sin. Kana, binciken da ta yi a shekarar 2026 ya nuna cewa, sun gamsu da yanayin kasuwanci na kasar Sin. Haka zalika kuma, kamfanonin suna ganin cewa, akwai damammaki masu kyau cikin kasuwannin kasar Sin, kana, sama da rabinsu, sun cimma riba sakamakon harkokin kasuwancin da suka yi a kasar Sin. (Mai Fassara: Maryam Yang)
[ad_2]
Source link