An kammala kaɗa ƙuri’ar zaɓen magajin Khamenei

[ad_1]



Majalisar ƙoli ta malaman addini da ke da alhakin zaɓen sabon jagoran ƙasar Iran ta ce ta riga ta yanke hukunci kan wanda zai gaji kujerar, amma har yanzu ba a bayyana sunansa ba.

Mamba a cikin majalisar, Ahmad Alamolhoda, ya ce an riga an kaɗa ƙuri’ar zaɓen sabon jagoran, kuma an cimma matsaya kan wanda zai hau kujerar.

Sai dai ya ce sakatariyar majalisar ce za ta sanar da sunan wanda aka zaɓa nan gaba.

Wasu mambobin majalisar sun tabbatar da cewa an riga an yanke shawara, inda ɗaya daga cikinsu ya nuna yiwuwar ɗan marigayi jagoran ƙasar, Mojtaba Khamenei, zai gaji kujerar mahaifinsa.

Mojtaba dai ɗan Ali Khamenei ne, wanda ya zama jagoran ƙasar tun shekarar 1989.

Muƙamin jagoran addini na Iran shi ne mai mafi girman iko a harkokin siyasa da addini a ƙasar, kuma shi ne ke da ikon yanke hukunci kan muhimman batutuwan gwamnati.

Wani mamba na majalisar daga lardin Khuzestan, Mohsen Heydari, ya ce mafi dacewa daga cikin ‘yan takarar ne aka zaɓa bayan samun rinjayen ƙuri’u.

A bayan nan dai Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sha nanata cewa yana son ya taka rawa wajen zaɓen sabon jagoran, inda kuma ya yi watsi da yiwuwar Mojtaba Khamenei ya gaji kujerar, yana mai cewa bai cancanta ba.

Sai dai jami’an Iran sun yi watsi da wannan batu, suna mai cewa Amurka ko wata ƙasar ba ta da wani tasiri a kan zaɓen sabon jagoran ƙasar.

Aminiya ta ruwaito cewa marigayi Ayatollah Ali Khamenei ya mutu ne a ranar 28 ga Fabrairu bayan hare-haren haɗin gwiwa da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan Iran, lamarin da har kawo yanzu ke ci gaba da rura wutar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Tarihin muƙamin jagoran addini na Iran

Mutumin da ya fi kowa iko a Iran shi ne jagoran addinin ƙasar tun bayan juyin juya-halin ƙasar da aka yi a 1979 da aka hamɓarar da mulkin sarauta ta Mohammad Reza Pahlavi.

Zuwa yanzu ƙasar ta yi jagororin addini guda biyu — Ayatollah Ruhollah Khomeini (wanda ya assasa Jamhuriyar Musulunci a ƙasar) sai wanda ya gaje shi, marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

Shi ne jagoran ƙasa kuma babban kwamandan tsaron ƙasar. Yana da iko a kan rundunar ’yan sanda da kuma jami’an Hisbah na ƙasar.

Jagoran addinin ne kuma yake da iko a kan dakarun juyin juya-hali ta ƙasar, wadda ita ce rundunar da ke kula da harkokoin tsaro na cikin gida, tare kuma da ɓangarenta na sojojin sa-kai da ake kira Basij.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *