2027: Dole Dattawan Arewa Su Hada Kai Domin Samar Wa Yankin Mafita —Alhaji Babangida Aliyu
[ad_1]
A karshen makon jiya ne Editanmu Bello Hamza ya tattauna da Alhaji Babangida Aliyu Bushiyarewanda kuma masani na tarihin yadda aka gudanar da Mulki a shekarun baya, a tattaunawar ya mayar wa da mai martaba Sarkin Gwandu mai murabus Alhaji Mustapha Jokolo martani a kan wasu maganganun da ya yi, musamman a kan bayanan da yi a kan Marigayi Mahmud Tukur a kan dangantakarsa da marigayi Tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga dai yadda hirar ta kasance:
Za mu so ka gabatar mana da kanka?
- INEC Ta Amince Da Shugabancin PDP Tsagin Wike
- Kwankwaso Bai Je Ƙasar Waje Neman Magani Ba – Kwankwasiyya
Ni suna na Aljhaji Babangida Aliyu Bushiyare, ni mutumin Yola ne ta Jihar Adamawa.
Me za ka ce game da bayanai da kuma korafi da tsohon Sarkin Gwamdu Alhaji Mustapha Jokolo ya yi a kan shugabannin Arewa?
Abin da ya faru na zo na gani a soshiyal midiya lallai Mai Martaba Sarkin Gwandu mai murabus Alhaji Mustapha Jokolo, ya yi jawabi kusan awa daya. A cikin jawaban da ya yi ya ambata sunanyen wasu shugabanni na Arewa. Ni abin da ya dame ni, nake son na mayar da martani, abu biyu ne ko uku. Na daya dai; a kan Dakta Mahmud Tukur; abin da ya ce Mamudu yana tare da gwamnatin Buhari, kuma sune suka bayar wa Buhari gurguwar shawara na shekara takwas; wannan sam, wannan ban yadda ba. Wannan sam ba haka ba ne. Shi Sarki ya san waye Mahmud Tukur; akidar Mahmud Tukur, da abin da Mahmud Tukur ya yi wa kasarnan musamman arewacin Nijeriya.
Mahmud Tukur mutum ne da Allah ya ba mutunci da kuma hikimar yadda za a hada kan mutane a samu mafita. Wanda shi Sarki da kansa ya sani, yana Gwandu yana barin Gwandu ya zo Kaduna su yi ‘meeting’ kuma su duba halin da Nijeriya ke ciki da yadda ‘yan Arewa za mu hada kan mu. Kafin na ci gaba, Mahmudun nan ina mai tabbatar maka, shi mutumin marigayi shugaban Buhari ne kwarai da gaske, da su Mamman Daura, su makusantan juna ne, babu tantama a kan wannan. Amma a cikin gwamnatin nan na shekara takwas, ina mai tabbatar maka sau biyu Mahmud ya zo Billa. Na dayan shi ne yayin rashin lafiyar Buhari, daga dawowar sa, Mahmud ya je ya gaishe shi. Na biyu lokacin da matarsa ta yi babatu a BBC, duk kan ku kun san hirar, nan ne ‘pressure’ ya yi yawa aka ce ya zo, ya je suka yi abubuwan su. To banda wannan babu wani abu. Ya ce su Mahmud sun yi ‘running’, yaushe Mahmudun ya yi ‘running’ gwamnati? A ina ta ina?
Wane kira kake da shi?
A kan haka ne nake kiran tsohon Sarki don Allah a matsayinsa ya janye wadannan kalaman nasa a kan Mahmud domin ba haka ba ne. Ya yi aiki da Mahmud. Shi da kansa ya taba fada tsohon Sarki cewa; Mahmud ne lokacin da suka yi gwamnatin shi wata ashirin, 1984-85; Mahmudu da shi da Rafindadi da shi suka yi ‘running’ gwamnatin Buhari ‘successful’. Aka tabbatar da shi, sannan yau ya ce mene ne? Ta ina? Wani yaron Mahmuda ya yi aiki a wajen?
Ta ina? Sannan ya ce su Mahmudu ne har ya yi ‘misleading’ su Janaral na mu; Janar Shehu Yar’adua, Janaral Babangida, da Buhari saboda ba su da ‘edperience’ din siyasa? To ina tabbatar ma Sarki da duk jama’a ta ‘president’ wannan, babu; ‘system’ mutum a duniya a Nijeriya wanda za ku samu kamar Janar Shehu ‘Yar’adua; Shehu ya yi ‘archiebing’, an sani, sai yau kuma an sani ‘on record’, amma ba abu ne da za a yi bayani sosai ba. Wannan a gurguje ne sama-sama nake kawo maka.
Babangida duk wani ya sani, Babangida mutum ne ‘a political leader’ babu wanda bai san waye Babangida ba a fagen siyasa ba. Yau idan abu zai faru sai kowa ya gudu ya je Minna, ana ‘pilgrimage’ a Minna. Buhari kuma yadda yake faruwa, kowa ya san waye Buhari; ta ya Buhari yake? Mamman da ake fada, Mamman, Mamman, ba wanda ba ya jin tsoron Buhari. ‘Buhari is in his own world’. Amma ba abu ne da za a yi magana ba.
To ni babban abu ina so tsohon Sarki, don Allah Mai Martaba ya sake duba ‘Archibe’ dinsa ya ga wane ne Dakta Mahmud. Maganar da ya yi din nan, kila yana a fusace ne. Idan mutum ya yi fushi, ba abin da ba zai fada ba. To ya sake duba wannan, domin bah haka Mahmud yake ba. Ya san waye Mahmud, ya kuma san mene ne gudummawar da Mahmud ya bayar. Sannan Mahmud bai shiga wancan gwamnati ba. Na shekaru 20 da Mahmud, ya shiga cikin gwamnati wasu sun kare, shima ba ya nan. Da abubuwan da Mahmud ya yi a nan din nan an yi. Da yake ni mutumin Mahmud ne. Kuma Mahmud ya rasu baya nan, sannan a yi masa wannan kage, ina ga ba a masa adalci ba.
Wannan shi ne babban abin da ya sa na ce bari na fita na fada wa Mai Martaba Sarki, don Allah ya koma ‘archibe’ dinsa ya duba. Ba haka Mahmud yake ba.
Me kake tunanin shi tsohon Sarki yake son ya cimma da wannan bayanan da ya fito da su yanzu?
Bayanan da Sarki ya fito da su; ka san duk lokacin da ake so a yi gyara, idan ka ce za ka kawo wasu surutai da maganganu, kuma gyaran ba zai taba yiwuwa ba. Wannan shi ne ni abin da nake so a nan; Sarki ya yi maganganu da yawa, babu wanda bai taba ba. Yau an ji maganganu mutanen mu na Arewacin Nijeriya suna yi kullum, to ‘the best’ abin da za a yi shi ne; mene ne ‘way forward’? Yanzu ga halin da muka tsinci kanmu; me ya kamata a yi? Shi shawarar da zan ba Sarki shi ne ya yi damara, ya zama kamaar Nelson Mandela, ya zama ‘unified leader’, ya nemo irinsa mu zauna, ko su zauna; me ya kamata a yi? Ga yadda muka tsinci kanmu a Nijeriya, ga yadda arewacin Nijeriya ya shiga, mai ya kamata a yi? Domin duk rigimar maganganu din nan, saboda zaben 2027 ne; mene ne ya kamata a yi? Mutane kar mu yi abin nan; mu buya a bayan gaskiya ana karya. Mu fuskancin gaskiya, 2027 di nan; mene ne abu biyu ne; yadda aka yi Muslim-Muslim ticket aka kawo ni Tinubu, yadda aka yi waye, to ga Tinubun; a abin da aka yi men ne aka yi aka samu? Ya za a yi wannan abu? Shin shi za a sake yi? A sake magana da shi, idan shi za a yi a yi. Idan kuma wannan abu ba za a canja ba, a kawo mana ka’ida, su kawo mutanen Kudu, su kawo mutanen Arewa; mu hadu mu fuskanci zahiri, amma ba a rika kananan maganganu ba. Muddin muna kananan maganganu ba za mu taba hada kanmu ba.
Mandela da ya zo ya fita ya ce kowa wanda aka raunata ne, a yi hakuri, a zo tebur a yafi juna. Shiyasa nake cewa Sarki tunda ya ambaci wannan, shi shugaba ne, mutumin kirki ne, ina girmama Sarki sosai, yana daya daga cikin mutanen da nake gani da gashi a kasar nan, da shi da Almustapha, da Nasir El-Rufai, irin su ina girmama su. Da su Abdullahi Isa, ina girmama su sosai. Ya hada su duka mu gani mu fuskanci zahiri, amma da ya ce; idan ba a yi hankali ba, masifar da yake gaban mu nan.
To tunda sun hangi masifa, ya zo ya zauna mu nemo mutane mu fuskanci zahiri. Kananan maganganu ba zai kai kowa ko’ina ba. Maganar kuma da ka tambaye ni, da ka ce me nake hanga? Idan na ce zan amsa zan yi bayani sosai, kuma zan yi ‘creating more problem’ ne. Duk lokacin da za ka cire haushi, haushi ne za ka kara. Sai a yi hakuri. Babban abu shi ne a yi gyara abin da aka ce kan Mahmud Tukur; na fada wa duniya, na fada masa ya sani ba haka ba ne. Kuma wanda ya ce Mahmud ya shiga gwamnatin (Buhari) na shekaru takwas, da shi aka ci gwamnatin, to ya kawo hujja. Yaronsa ya yi gwamnatin, ya kawo hujja, wani kwangila Mahmuda ya samu, ya kawo hujja.
Duka wadannan babu, yanzu to ya ya za mu hada kan mu mu yi ‘reconciling’ mu zana tsintsiya madaurinki daya. Mu hada kan mu mu fuskanci matsalolin nan. Tunda Sarki ya kawo wannan, ni na yadda ya zo ya zame mana Nelson Mandela din mu; ya hada kanmu.
Ka san idan mutum soja ne, sannan ya yi fushi, yana magana, yadda yake magana din sai dai a ce Allah ya ba shi hakuri. Amma dole ne a yi hakuri, saboda ‘inedperience’ da mene ne, ba mu hada kan ba, kuma kowa a lokacin ma zai iya fada. Saboda akwai lokacin da Sarki ya fita ya ce abin da ake yi a gwamnatin Buhari din nan ba haka ba. Saboda haka yanzu din nan lokaci ya zo nan da wata shida, mu hada kan mu wuri daya ba zargi ba. Kowa ya san me ya kamata a yi. A shekarar 1979, Shehu Shagari ya nemi shugaban kasa ne? Ai an zauna a tebur ne, wadanda suke nema, aka ce zauna. A nemo mutanen Kudu a nemo mutanen Arewa, mu fuskanci zahiri. Idan kuma a za a yi ‘reconciling’ da gwamnatin Tinubu, a samo Tinubu; a shaida masa cewa mu muka yi ka, ga yadda kuma muka yi, ga kuma yadda muke gani yadda tafiyar nan yake; Arewacin Nijeriya ta mutu; ya ya za a yi? Idan bah aka wallahi ba za a yi ba. Mu fuskanci zahiri, daga nan zai kare ai? Wani abu ne? Waye bai yi ba? Namarudu ma ya yi ya tafi ai.
A yi haka a fuskanci zahiri. Mu daina yi wa kan mu karya, idan ba haka ba, ba inda za mu je. Sai duk gwamnonin sun ce sun koma, ta ina? Kuma karya ne? Shugabanci babu wanda za su yi, abin haushi ka rasa yadda zaka yi. To tunda Mai Martaba ya fita, ni dai na yi masa jinjina, kuma na ba shi ‘support’ na ‘5 to 6’ in ji Bature, mu mutanensa ne, ya yi yadda za a yi a hada ‘team’, mu yi ‘facing reality toward 2027’, domin duk maganar nan ta zaben 2027. Ka da mu yi boye-boye muna yi wa junan mu karya. Mu fuskanci zahiri kawai; su waye ya kamata a zauna da su a kan tebur, kowa ya san kima ai. Kai ka san matsayin waye ya kamata ya zamto kaza, wannan ya cancanci matsayi kaza. Amma a bar yi a gurguje wani dan lido ya ce ma shi ne kaza. Ka duba mutanen Arewancin Nijeriya din nan, kamar yadda yake magana; su Sanatoci, su wane ne, kowa ya yi shiru, ba mai magana; a hada ma a je a samu shugaba Tinubu ma ya gagara, to muddin idan ba a samo irin Sarki yadda yake ta yi din nan, ya samo irin su a zauna mu fuskanci zahiri, ba inda za mu je. Wannan shi ne matsayina.
Mun gode sosai
Nima na gode
[ad_2]
Source link