An kama Mai Unguwa kan yi wa yarinya fyaɗe a Gombe
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe ta kama wani Mai Unguwa mai shekara 55 a garin Zambuk da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba, bisa zargin yi wa wata yarinya ’yar shekara 12 fyaɗe.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar, DSP Buhari Abdullahi ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya bayyana wanda ake zargin Mohammed Tukur da ke ƙauyen Sabon Gari da ke Zambuk.
A cewar rundunar ’yan sandan, lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Agusta, da misalin ƙarfe 9 na dare, inda ake zargin Mai Unguwar ya yaudari yarinyar (wacce aka sakaya sunanta) zuwa wani keɓantaccen wurin da aka aikata laifin.
Ya ce, “Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda na ofishin ‘yan sanda na Zambuk sun yi gaggawar zuwa wurin, inda suka kuɓutar da yarinyar, suka kai ta babban asibitin Zambuk, domin a duba lafiyarta.
“An kama wanda ake zargin kuma an tsare shi nan take.”
Kakakin ’yan sanda PRO ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ya jaddada ƙudirin rundunar na tabbatar da yin adalci ga wacce aka yi wa fyaɗen.
Ya yi Allah-wadai da wannan aika-aika tare da yin kira ga mazauna garin da su gaggauta kai rahoton duk wani abin da ya faru na lalata domin samun damar shiga tsakani na ’yan sanda kan lokaci.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link