Duk Da Rashin Nasara A Hannun Morocco, BUA Ya Bai Wa Super Eagles Kyautar Dala 500,000

[ad_1]

Attajirin dan kasuwa kuma shugaban kungiyar BUA, Abdulsamad Rabiu, ya yaba da rawar da Super Eagles ta taka a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin kasashen Afirka (AFCON) da Morocco mai masaukin baki, yana mai cewa kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ta buga duk abin da ya dace ta buga kuma ta nuna jarumtaka a wasan.

Da yake magana a shafinsa na sada zumunta jim kadan bayan wasan da Nijeriya ta yi rashin nasara a hannun Morocco a bugun fanateti, wanda ya kare da ci 4:2, dan kasuwar, wanda a baya ya yi wa Super Eagles alkawarin kudi mai yawa idan suka lashe wasan, ya ce har yanzu yana kan batunsa wajen cika alkawarin kyautar dala 500,000 a matsayin godiya ga ‘jarumta da kokarin da kungiyar ta yi’.

  • Gwamnatin Kaduna Ta Ce Shari’ar Zidan Ta Gudana Cikin Gaskiya da Adalci
  • An Yi Bikin Murnar Kaddamar Da Shekarar Musayar Al’adu Da Cudanyar Jama’a Ta Sin Da Afirka A Afirka Ta Kudu

LEADERSHIP ta rahoto cewa, jim kaɗan bayan ta doke Algeria da ci 2:0 a wasan kusa da na kusa da na ƙarshe na AFCON na 2025 a ranar Asabar, Abdulsamad Rabiu ya yi alƙawarin ba wa Super Eagles $500,000 bayan sun lashe wasan kusa da na ƙarshe na ranar Laraba da ƙarin $50,000 ga kowace kwallo da aka ci, da kuma kyautar dala miliyan 1, idan Super Eagles ta ci kofin AFCON a wasan ƙarshe. Amma hakan ba ta yi wu ba.

Da yake magana kan wannan alkawarin da ya ɗauka jim kaɗan bayan fafatawa a wasan na kusa da na ƙarshe, Rabiu ya ce, wani lokacin, ƙoƙari baya kawo sakamakon da ake fata, amma ruhi, sha’awa, da haɗin kai da aka nuna wajen cimma fatan, su ne abin da ke da muhimmanci.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *