’Yan bindiga sun kai sabon hari tare da kashe tsohuwa mai shekaru 75 a Neja

[ad_1]



’Yan bindiga sun kashe wata tsohuwa ’yar shekaru 75, mai suna Amina Abu-Shaki a ƙauyen Kabe da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja.

Sun kashe matar ne a daren ranar Talata, lokacin da maharan suka kai hari.

’Yan bindigar sun kai harin ne da misalin ƙarfe 8 na dare, inda suka riƙa harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa, suka fasa shaguna, suka kwashe kayan abinci da dukiyoyi.

Ba su yi garkuwa da kowa ba a lokacin da suka kai harin.

Wani mazaunin ƙauyen, Mallam Awwalu, ya ce ƙauyuka da dama a yankin sun zama kufai saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

A wani hari kuma, ’yan bindiga sun kashe mutane huɗu a ƙauyen Damala, wanda shi ma ke Ƙaramar Hukumar Borgu, a ranar Juma’a.

Sun kuma sace shanu da dabbobi, tare da ƙone gidaje da wuraren ibada.

Jami’in kula da iftila’i na Ƙaramar Hukumar ya tabbatar da mutuwar mutanen huɗu.

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya umarci al’ummar da ke kewaye da Tafkin Kainji da su bar gidajensu nan da watanni biyu.

Wannan na da nufin bai wa jami’an tsaro damar yaƙar ’yan bindiga da ke ɓoye a yankin ba tare da cutar da fararen hula ba.

Sarkin Borgu, ya ce masarautar za ta haɗa kai da hukumomi domin gano tare da hukunta masu bai wa ’yan bindiga bayanai.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *