Gwamnatin Kano Ta Rushe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Ta Haɗe Ta Da Ma’aikatar Ilimi

[ad_1]

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da haɗe Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi da Ma’aikatar Ilimi a wani mataki na sake fasalin tsarin gudanar da ilimi a jihar.

Sanarwar wacce mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu ranar Lahadi ta bayyana cewa bayan wannan sauyi, sabuwar ma’aikatar za ta ci gaba da aiki da sunan Ma’aikatar Ilimi, inda za a kafa wani sashen kula da Ilimi Mai Zurfi a cikinta domin sa ido kan jami’o’i da sauran cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare.

  • Kwankwaso Bai Taɓa Neman Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa Ba – NNPP
  • Shugabar ALGON Ta Kano Ta Buƙaci Dakatar Da Aiyukan Siyasar Ado Doguwa

Sanarwar ta kara da cewa dukkan hukumomi da ke ƙarƙashin tsohuwar Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, ciki har da Kano State Scholarship Board, za su koma ƙarƙashin Ma’aikatar Ilimi, yayin da jami’o’in gwamnati da sauran manyan cibiyoyin ilimi za su kasance ƙarƙashin sabon sashin kula da Ilimi Mai Zurfi.

Gwamnatin jihar ta ce wannan mataki na daga cikin shirin gyaran ɓangaren ilimi domin rage maimaituwar ayyuka, da inganta haɗin kai wajen tsara manufofi da kuma rage kashe kuɗin gudanar da gwamnati.

Gwamna Yusuf ya jaddada cewa sauyin zai taimaka wajen ƙara inganci da gaskiya a tafiyar da ɓangaren ilimi tare da tabbatar da cewa ana aiwatar da manyan sauye-sauye da za su farfado da ilimi a jihar domin amfanin matasa na gaba.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *