Masanin Zimbabwe: Manufar Soke Harajin Kasar Sin Ga Afirka Za Ta Kara Habaka Fitar Da Kayayyaki Zuwa Ketare
[ad_1]
Wani masani na kasar Zimbabwe ya bayyana cewa, manufar soke harajin kwastam ta kasar Sin ga kasashen Afirka 53, za ta bayar da damammaki ga ‘yan Afirka masu fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare.
Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ranar Jumma’ar da ta gabata, mai fashin baki kan harkokin tattalin arziki na kasar Zimbabwe, kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Dereck Goto, ya ce, manufar tana nuna gagarumin sauyin tsarin dangantakar cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka.
A watan Fabrairun da ya gabata, kasar Sin ta sanar da cewa, za ta fara cikakkiyar aiwatar da manufar soke harajin kwastam ga kasashen Afirka 53 masu huldar jakadanci da ita daga ranar 1 ga watan Mayun bana.
Goto ya ce sabon matakin da kasar Sin ta dauka na da matukar muhimmanci a fannin siyasar yankuna. Ta hanyar bayar da damar soke biyan harajin kwastam a sassan nahiyar Afirka, kasar Sin tana kara karfafa matsayinta na abokiyar kasashe masu tasowa, tare da bude hanyoyin samun ci gaba masu tushe na cinikayya.
Ya kara da cewa, “A takaice dai, ga kasar Zimbabwe da sauran abokan hulda na Afirka, manufar soke harajin kwastam ta zarce wata alama ta karamci. Gayyata ce ta zurfafa karfin masana’antu, da fadada fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje da kuma tabbatar da hadewa da daya daga cikin manyan kasuwannin tattalin arzikin duniya. Babban abin da ya fi zama mai muhimmanci a yanzu shi ne yadda masu samar da kayayyaki na Afirka kimtsa kansu yadda ya kamata domin cin gajiyar damar da aka samu.” (Abdulrazaq Yahuza Jere)
[ad_2]
Source link