Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250 a Jami’ar Ilorin
[ad_1]
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.
Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.
Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Ya ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.
Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.
AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.
Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.
Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link