Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai

[ad_1]



Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bai wa Gwamnatin Tarayya ranakun 24, 25 da 26 ga watan Satumba domin ta kammala shari’ar da ta shafe shekaru goma tana yi wa tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, kan zargin mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗin haram.

Mai shari’a Peter Lifu ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata, bayan amincewa da buƙatar gwamnati ta ɗage zaman domin kawo ƙarin shaidu da kuma ba wa Dasuki damar fara kare kansa.

Ya kuma umurci gwamnati ta kira sauran shaidunta domin kammala gabatar da shaida a shari’ar da aka shafe fiye da shekaru goma.

Tun a shekarar 2015 aka kama Dasuki bisa zargin karkatar da dala biliyan 2.1 na kuɗin sayen makamai, inda ya samu ’yanci a ranar jajiberin Kirsimetin shekarar 2019, bayan ce-ce-ku-ce kan ƙin bin umarnin kotuna da dama, ciki har da na Kotun Ƙoli ta ECOWAS, wadda ta ba shi beli.

A zaman da ya gabata, wani mai ba da shaida daga bangaren gwamnati, Monsur Mohammed, wanda shi ne mai kula da kayayyakin shaida a Hukumar Tsaro ta DSS, ya shaida wa kotu cewa jami’an tsaro sun yi bincike a gidajen Dasuki da ke Abuja, Kaduna da Sakkwato bayan cafke shi.

Haka kuma, Dasuki yana fuskantar wata shari’a ta daban a Babbar Kotun Abuja wadda hukumar EFCC ke zarginsa da karkatar da kuɗin makamai na Naira biliyan 19.4.

Sauran wadanda EFCCn ke tuhuma tare da Dasuki sun haɗa da tsohon Ministan Harkokin Kuɗi, Bashir Yuguda, tsohon Gwamnan Sakkwato, Attahiru Bafarawa, da ɗansa Sagir, da kamfaninsu, Dalhatu Investment Limited.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *