Tinubu Ya Bai Wa Masu Riƙe Da Muƙamai Da Ke Son Yin Takara Wa’adin Yin Murabus
[ad_1]
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci duk masu muƙaman gwamnati da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 su ajiye muƙamansu kafin ranar 31 ga watan Maris, 2026.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa daga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, wadda George Akume ya sanya wa hannu.
- Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Ƙaramar Salla
- El-Rufai Ya Zargi ICPC Da DSS Kan Tsare Shi Ba Bisa Ƙa’ida Ba Da Neman Ya Yi Ritaya Daga Siyasa
Umarnin ya biyo bayan dokokin zaɓe da jadawalin zaɓe da INEC ta fitar.
Umarnin ya shafi ministoci, masu bai wa shugaban ƙasa shawara, mataimaka na musamman, shugabannin hukumomi da sauran masu muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara.
Dukkanin waɗanda abin ya shafa dole ne su miƙa takardun murabus ɗinsu ta hannun ofishin sakataren Gwamnatin Tarayya kafin wa’adin da aka ƙayyade.
Tinubu ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin tabbatar da adalci, bin doka, da kuma bai wa kowa damar yin takara cikin gaskiya.
[ad_2]
Source link