Kotu A Norway Ta Ɗaure Ɗan Wasan Nijeriya Kan Zargin Aikata Fyaɗe

[ad_1]

Wata kotu a ƙasar Norway ta yanke wa ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Nijeriya, Daniel Daga, hukuncin ɗaurin watanni shida a gidan yari bayan ta same shi da laifin yin lalata da wata mata ba tare da izininta ba.

An bayyana hukuncin ne a ranar Talata, inda kotun ta kuma umarci ɗan wasan mai shekaru 19 da ya biya tarar Kroner 10,000 na kuɗin Norway.

  • Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda 3, Sun Ƙwato Makamai A Sakkwato
  • Gwamnati Ta San Sunaye Da Wuraren Da ‘Yan Ta’adda Suke — Sheikh Gumi

Gidan talabijin na Norway, TV 2, ne ya ruwaito hakan.

Rahoton ya ce hukuncin da kotun ta yanke ya yi daidai da abin da mai gabatar da ƙara ta nema.

Sai dai lauyan Daniel Daga, Astrid Bolstad, ya ce ɗan wasan ya yi matuƙar takaici da hukuncin, kuma ya dage cewa bai aikata laifin da ake tuhumarsa da shi ba.

Bolstad ya ce Daga yana cikin damuwa matuƙa saboda hukuncin, kuma yana ganin abin da ya faru tsakaninsa da matar ya kasance da yardarta.

Lauyan ya ƙara da cewa ɗan wasan na shirin ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun.

A wata sanarwa da ƙungiyar kwallon kafa ta Molde ta fitar daga baya a ranar Talata, ta ce ba za ta saka Daga cikin ‘yan wasan da za su buga wasan ƙungiyar a wannan makon ba, saboda hukuncin da kotu ta yanke masa.

Daniel Daga ya koma ƙungiyar Molde kafin fara kakar wasa ta 2025, kuma ya buga wasanni 15 inda ya zura ƙwallaye uku.

Kafin komawarsa Turai, Daga ya taɓa buga wa ƙungiyar Enyimba wasa a gasar Firimiyar Nijeriya.

A matakin ƙasa da ƙasa kuwa, ya taɓa wakiltar tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya ta ‘yan ƙasa da shekaru 20, inda ƙoƙarinsa ya ja hankalin manyan ƙungiyoyin Turai kafin daga bisani ya koma Molde FK.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *