Yadda Yara Suka Kamo Harsasan Harbo Jirgin Sama A Yayin Kamun Kifi A Borno

[ad_1]

Wata ragar kama kifi da wasu yara suke amfani da ita wajen kama kifaye a wani kududdufi a yankin Bulunkutu na Maiduguri, Jihar Borno, ta nannaɗo harsasan harbo jirgin sama a yayin kama kifaye a kududdufin.

Majiyoyi a yankin sun yi zargin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram ne suka jefar da harsasan.

  • Gwamnonin Arewa Sun Yi Allah-Wadai Da Harin Kasuwar Neja
  • Tinubu Ya Yaba da Jagorancin Gwamna Abba Yusuf Yayin Da Ya Cika Shekara 63

Wata majiya ta ce lokacin da yaran suka lura da abubuwan da suka kamo, ba a bu bane da aka saba gani ba, sai suka sanar da hukumomi, wanda ya sa sojoji suka killace yankin da sauri.

Wata majiya ta shaida wa wakilin Daily Trust cewa, “Yaran ƙanana ne. Babban cikinsu, bai wuce shekaru 13 ba. Yawanci suna kamun kifi a wurin ne don kama ƙananan kifaye yayin da ruwan kududdufin ya fara ƙafewa. Amma a wannan karon, maimakon kifi, sai suka kwaso harsasai da dama da kuma abubuwan ajiyar wutar lantarki na hannu (power Bank), lamarin da ya tsorata kowa a yankin.”

Wani mazaunin garin, wanda ya bayyana sunansa a matsayin Malam Bishir, ya ce, “Abin da ya firgita yawancin mazauna yankin shi ne, tarihin wurin. Wasu sanannun ‘yan Boko Haram sun taɓa zama a wurin kafin rundunar tsaro ta hadin gwiwa (CJTF) ta kore su.”

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake fargabar tsaro a Borno da jihohin Yobe da Adamawa da ke makwabtaka da juna, inda aka samu munanan hare-haren fashewar bama-bamai da kuma dakile hare-haren ƙunar baƙin wake a cikin ‘yan makonnin nan.

Sai dai, an rahoto cewa, sojojin Operation HADIN KAI (OPHK) sun kama wanda ake zargi da jagorantar kai hare-haren bama-baman wanda ya kashe mutane biyar tare da raunata wasu 34 lokacin da wani ɗan ƙunar baƙin wake ya tayar da bam a cikin wani masallaci a Maiduguri.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *