Saudiyya Ta Rage Samar Da Man Fetur Saboda Matsalar Jigila A Hormuz

[ad_1]

Saudiyya ta rage yawan man fetur da take samarwa saboda matsalar jigilar kaya ta ruwa a kogin Hormuz, sakamakon rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Sauran ƙasashen da ke cikin ƙungiyar OPEC kamar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Kuwait da Iraq su ma sun rage yawan man fetur da suke samarwa.

  • SAHUR (Falalarsa Da Fa’idojinsa) Na 22
  • Jami’an Tsaro Sun Kashe ‘Yan Bindiga 5 A Jihar Zamfara

Masana sun ce Saudiyya ta rage samar da man tun da wuri domin kada tankunan ajiyarta su cika, tare da tabbatar da cewa rijiyoyin man nata na ci gaba da aiki ba tare da an rufe su gaba ɗaya ba.

A kullum Saudiyya na samar da kusan ganga miliyan 10 na man fetur, kuma tana fitar da kusan ganga miliyan bakwai zuwa ƙasashen waje.

Saboda wahalar wucewa ta mashigar Hormuz, Saudiyya na karkatar da wasu daga cikin man zuwa Yanbu ta hanyar bututun mai da ya nufi Red Sea.

Sai dai wannan bututun na iya ɗaukar ganga miliyan biyar ne kawai a rana, wanda bai kai yawan man da ake fitarwa ba.

Wannan matsala ta sa farashin man fetur a duniya ya haura dala 100 kan kowace ganga, tare da jawo matsaloli a harkokin samar da shi a duniya.

Masana sun yi gargaɗin cewa idan rikicin ya ci gaba, zai iya jawo hauhawar farashi a duniya.

A halin yanzu kamfanin man fetur na ƙasar, Saudi Aramco, bai fitar da wata sanarwa ba kan lamarin, yayin da yawancin jiragen ruwa masu ɗaukar man fetur ke gujewa wucewa ta mashigar Hormuz saboda dalilan tsaro.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *