Binciken CGTN: Shawarar Inganta Wayewar Kai A Duniya Ta Kasar Sin Na Kawo Zaman Lumana Ga Duniya Mai Cike Da Hargitsi

[ad_1]

Yayin da al’ummomin kasa da kasa, a yanayi mai sarkakiya da hargitsi ke cikin wani hali na sauye-sauye masu zurfi da ba za a iya hasashe a kai ba, shawarar inganta wayewar kai a duniya da kasar Sin ta gabatar tana kawo zaman lumana ga duniya mai cike da tashin-tashina.

Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN tare da Jami’ar Renmin ta kasar Sin suka gudanar ta hannun Cibiyar Nazarin Sadarwa ta kasa da kasa ta New Era, wanda ya kunshi mutane 12,302 daga kasashe 41 na duniya, ya nuna cewa, wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu sun yi magana mai kyau game da shawarar inganta wayewar kai a duniya da kasar Sin ta gabatar.

Gaba daya sun yi amannar cewa ainihin ra’ayoyin da shawarar ta kunsa, kamar mutunta bambancin wayewar kai da inganta kyawawan dabi’un dan’adam na gama-gari, suna da ma’ana mai matukar muhimmanci a yanayin kasa da kasa da ake ciki yanzu.

Kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen sakin mara ga mu’amalar al’adu ta yadda za ta kawar da bakonta, da yadda koyo daga juna zai maye fadace-fadace, kana da yadda zaman tare zai maye jiji-da-kai ko ganin fifiko a kan wasu. A cikin binciken, kashi 90.8% na masu bayyana ra’ayoyi sun yi amannar cewa mutunta bambance-bambancen wayewar kai, muhimmiyar ka’ida ce da ta kamata kasashen duniya su bi.

Haka nan kashi 77.2% na masu bayyana ra’ayoyin sun yarda cewa babu wata wayewar kai da ta fi wata. Sannan kashi 87.7% sun ce ya kamata a rika tafiyar da duk wayewar kai bisa daidaito, kana daga cikin wadanda suka bayyana ra’ayoyinsu daga Afirka da yankin Amurka ta Kudu sun nuna amincewa sosai da daidaiton dukkanin wayewar kai, inda wadanda suka amince da hakan suka kai yawan kashi 93.1% da 90.3%, bi-da-bi.

A ko da yaushe kasar Sin ta yi amannar cewa, zaman lafiya, da ci gaba, da adalci, da dimokuradiyya da ‘yanci, su ne burika na bai-daya ga dukkan al’ummomi. A cikin binciken, kashi 91.8% na masu bayyana ra’ayoyin sun yarda da wannan ra’ayi sosai kuma suka ce ya kamata al’ummomi daban-daban su ba da fifiko ga hadin gwiwar samun nasara ga ko wane bangare a maimakon fito-na-fito da juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *