Yadda ’yan ta’adda suka kashe mutane 60 Neja
[ad_1]
Rahotanni daga Jihar Neja sun ce aƙalla mutane 60 ne ’yan bindiga suka yi wa kisan gilla a ƙarshen mako a yankin Ƙaramar Hukumar Borgu.
Mazauna yankin sun bayyana cewa adadin mamatan na iya ƙaruwa a yayin da ake ci gaba da aikin ceto da neman mutanen da suka ɓace bayan harin da aka kai a Kasuwar Daji da ke ƙaramar hukumar.
Wani mazaunin yankin, Mista Marcus Philips Adoka, a ya ce, “Kusan ƙarfe 5pm ranar Asabar muka ga tashin hayaƙi a kasuwar. Ba a iya nan abin ya tsaya ba, sun ta fi da mutane da dama, wasu muka sun jikkata.
“Jera mutanen suka yi suka yayyanka su kamar kaji da awaki. Gawar mutum 42 muka fara samu, ciki har da gawar Rabaran ɗin al’ummar.”
Wani mazaunin garin ya ce bayan ’yan ta’addan sun gama aika-aika a kasuwar, sun shiga cikin garin, inda suka riƙa riƙa kulle mutane a cikin ɗakuna, suna cinna wa gidajen wuta.
Sun kuma sace kayayyakin abinci da kadarori masu daraja a kasuwar sa’annan suka cinna mata wuta a aika-aikan kai safiyar Lahadi suna aiwatar da ta’addanci.
Wasu mazauna sun ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 60, a yayin da wasu ke ganin ya fi haka, kuma akwai yiwuwar adadin zai iya ƙaruwa.
Aminiya ta ruwaito cewar daga cikin waɗanda aka sace har da wasu daga cikin ɗaliban Makarantar Katolika da ke yankin Papiri da aka ceto su a kwanan nan bayan ’yan bindiga sun yi garkuwa da su.
Shaidu sun ce bayan kimanin awa 12 da faruwar lamarin, masu aikin ceto daga ƙauyuka maƙwabta sun yi ta gano ƙarin gawarwaki a cikin daji.
Sun bayyana cewa da farko a gano gawarwaki 47 da suka haɗa da Musulmi da Kirista, inda aka yi musa jana’iza aka binne su a tare manyan kaburbura da aka gina a ranar Lahadi.
Wani ya ƙara da cewa, “Sun kashe mutum 37 a Kasuwar Daji kusa da Papiri, mutum 5 a ƙauyen Kaima, sannan suka yi garkuwa da mutane da dama, ciki har da yara, wasu daga cikinsu ɗaliban St. Mary’s Catholic School da aka ceto kwanan nan.”
Daraktan Hulɗa da Jama’a na Cocin Katolika na Kontagora, Rabaran Stephen Kabirat, ya ce, “Limamin parishi ya tsira daga garkuwa lokacin da ’yan ta’addan suka kai hari gidan mishan ɗinmu kwanaki uku da suka gabata. Sun lalata kayan ibada, sun kwashe babura biyu da kuɗi N200,000. Sun nemi limamin, amma ya tsere. Sai dai sun yi garkuwa da wasu mazauna ƙauyen, ciki har da yara.”
Yankin da abin ya faru yana da kusanci da yankin Papiri da ke Ƙaramar Hukumar Agwara, inda a kwanakin baya ’yan ta’adda suka yi garkuwa da ɗalibai a Makarantar Katolika ta St. Mary a ranar 21 ga watan Nuwambar 2025.
Wasu mazauna sun ce adadin mutanen da suka mutu ya kai 60, a yayin da wasu ke ganin ya fi haka, kuma akwai yiwuwar adadin zai iya ƙaruwa.
Bayanin ’yan sanda
Kakakin ’yan sanda ta Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya ce, ’yan bindiga sun fito ne daga dajin National Park kusa da Kabe suka afka wa Kasuwar Daji. Sun ƙone kasuwa, sun fasa shaguna, sun kwashe kayan abinci.”
Ya ƙara da cewa a safiyar Lahadi, tawagar tsaro ta haɗin gwiwa ta kai ziyara wurin, inda aka tabbatar da mutuwar fiye da mutum 30, tare da yin garkuwa da wasu. Yanzu haka ana ci gaba da ƙoƙarin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
A watan Nuwamba 2025, bayan sace ɗaliban makarantar St. Mary’s a Papiri, Sarkin Borgu, Alhaji Muhammad Sani Haliru Ɗantoro, ya roƙi Gwamnatin Tarayya ta yi bincike a Kainji National Park, inda jama’a ke ta zargin ’yan ta’adda na fakewa.
Hare-haren baya-bayan nan
Yankunan Borgu, Agwara, Mariga, Rijau, Magama da Mashegu sun fuskanci hare-hare tun daga Oktoba 2025.
Daga 29 ga Satumba 2025 zuwa Janairu 2026, manoma da matafiya da dama aka kashe ko aka yi garkuwa da su, duk da cewa iyalai sun biya miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.
Cikin waɗanda aka yi garkuwa da su akwai Alhaji Alhassan Bawa Niworo, tsohon shugaban Hukumar Ilimi a Matakin Farko (SUBEB), da kuma Barista Ahmed, kwamishina a hukumar zabe ta NSIEC. An sace su a kan hanyar New Bussa–Mokwa a ranar 29 ga Satumba 2025.
Ɗan tsohon shugaban SUBEB, Saifullah Bawa Niworo, ya ce sun biya N30m da aka tara ta hanyar aro daga bankuna da gudunmawar jama’a, amma ’yan ta’addan sun nemi ƙarin N120m.
A ranar 21 ga Nuwamba 2025, sama da ɗalibai da malamai 200 na St. Mary’s Papiri aka yi garkuwa da su, daga baya ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro ya ceto su bayan makonni da dama.
A watan Nuwamba, ’yan ta’adda sun yi garkuwa da matafiya a hanyar Wawa–Luma, inda suka tare motocin fasinja biyu, suka yi garkuwa da dukkan fasinjoji.
A ranar 23 ga Disamba 2025, sun kai hari ga ofishin hukumar tsaro ta NSCDC a ƙauyen Ibrahim Leteh, suka lalata ofishin da motocin sintiri.
Umarnin Shugaba Tinubu
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci Ministan Tsaro, shugabannin rundunonin tsaro, su bi diddigin waɗanda suka kai harin Kasuwar Daji.
Ya ce dole ne a kamo su a gaggauce, a kuma ceto dukkan waɗanda aka yi garkuwa da su.
Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce, “Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin da aka kai Kasuwar Daji da kuma yin garkuwa da mata da yara. Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwa, da gwamnatin Jihar Neja.”
Shugaban ƙasa ya ƙara da cewa, “Waɗannan ’yan ta’adda sun gwada ƙarfin ƙasarmu da jama’arta. Dole ne su fuskanci cikakken hukunci. Duk wanda ya taimaka musu ko ya ɓoye su, za a kamo shi.”
Martanin gwamnonin Arewa
Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta yi Allah wadai da harin Kasuwar Daji, tana kiran shi azzalumci ga ’yan ƙasa marasa laifi da barazana ga zaman lafiya da rayuwar tattalin arziki.
Shugaban kungiyar, Gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya ce, “Kai hari ga ’yan kasuwa da mata a kasuwa abin kunya ne, kuma ya shafi haɗin kan al’umma da rayuwar tattalin arzikin yankin.”
Ya yi kira ga jami’an tsaro su ƙara ƙoƙari wajen kamo masu laifin tare da tabbatar da sun fuskanci hukunci.
Ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa ’yan uwa, da gwamnatin Jihar Neja, tare da addu’ar samun sauƙi ga waɗanda aka yi garkuwa da su.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link