Yau ake addu’ar kwana 40 da rasuwar Sheikh Ɗahiru Bauchi

[ad_1]



A yau Litinin 5 ga Janairun 2026 ake gudanar da addu’ar kwana 40 da rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Ɗan Marigayin, Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ne ya sanar da adduʼar wacce za a gudanar a masallacin Shehin da ke Bauchi.

Aminiya ta rawaito cewa Marigayin ya rasu a ranar 27 ga watan Nuwambar 2025 bayan an garzaya da shi Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa bayan kamuwa da rashin lafiya, inda ya rasu da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Marigayin ya rasu yana da shekara 101 a duniya.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *