An ƙaddamar da sabbin kayan bunƙasa kiwo




Ministan Bunƙasa Kiwon Dabbobi na Tarayya, Idris Mukhtar Maiha ya qaddamar da sabuwar cibiyoyin sarrafa iri na ciyar da dabbobi da kuma ma’ajiyar tanada busasshiyar ciyawa ta dabbobi (hay).

Ministan ya yi hakan ne lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya a Cibiyar Binciken Samar da Dabbobi da inganta su ta Kasa (NAPRI), da ke Shika -Zariya, a Jihar Kaduna.

Ziyarar na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na sake farfaɗo da ɓangaren kiwon dabbobi a Nijeriya domin ƙara yawan dabbobi da kuma amfanin gona da kuma tabbatar da wadatar abinci.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamarwar, Minista Idris Mukhtar Maiha ya bayyana cewa, an samar da waɗannan kayayyaki ne ta hannun Bankin Duniya na Shirin Tallafa wa Samarwa da inganta harkar kiwo (L-PRES), karkashin shirin ajandar  Shugaban Kasa ta ‘Sabuwar Nijeriya’ na (Renewed Hope Agenda).

Ministan ya ce, samar da kayayyakin suna cikin muhimman jarin da aka tanadar domin magance matsalolin da aka daɗe ana fuskanta, musamman game da wadatar abincin dabbobi, bunƙasa ciyawar kiwo da samar da ruwa don bunqasa dabbobi.

“Abinci da bunƙasa ciyawar kiwo na daga cikin muhimman ginshiƙai wajen inganta samar da amfanin kiwo a Najeriya.

Waɗannan kayayyaki an tanadar da su ne domin tallafa wa cibiyar NAPRI ta samar da mafita masu amfani, bisa buƙatar kasuwa, da za su ƙarfafa tsarin kiwon dabbobi tare da inganta wadatar abinci,” in ji shi.

Kayayyakin da aka qaddamar sun haɗa da: Ma’ajiyar busasshiyar ciyawa mai iya ɗaukar tan 500 a shekara, da kuma injin sarrafa irin ciyawar kiwo mai layi ɗaya da ke da ƙarfin sarrafa tan 10 a awa ɗaya, rumfar busar da irin ciyawar kiwo mai ƙarfin tan 20 a shekara, da rijiyoyin burtsatse guda huɗu masu amfani da hasken rana tare da matattarar shan ruwa a cikin NAPRI, da kuma ƙarin rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a ɗaya daga cikin rukunin cibiyar da ke Jihar Yobe.

Ministan ya yi kira ga ma’aikatan NAPRI da su yi amfani da waɗannan kayayyaki yadda ya dace, tare da ƙara zurfafa rawar da take takawa a matsayin cibiyar ƙwarewa ta bincike, ƙirƙira da yaɗa fasahohi a fannin kiwo.

“Dole NAPRI ta ci gaba da jagoranci wajen ƙirƙira da yaɗa sabbin dabaru da za su tallafa wa kiwon dabbobi don kasuwanci.

Burinmu shi ne ganin sakamakon bincike ya zama riba ga manoma, samar da ayyukan yi ga matasa, da inganta rayuwar ’yan Najeriya,” in ji Ministan.




Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *