Hatsarin Jirgin Ruwa: Adadin waɗanda suka rasu ya kai 60 a Neja
[ad_1]
Adadin mutanen da suka rasu a hatsarin jirgin ruwa da ya auku a yankin Malale, da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja, ya kai 60.
Jirgin ruwan, wanda ya ɗauko kusan mutum 90, ya tashi daga Tugan Sule a gundumar Shagunu, kuma yana kan hanyarsa ta zuwa Dugga.
Mutanen da ke cikin sun tafi yin gaisuwar ta’aziyya ne, lokacin da hatsarin ya auku a ranar Talata, 2 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 11:30 na safe.
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA), ta ce hatsarin ya faru ne akamakon dukan wani itace da ke cikin ruwa.
Da farko, an gano gawarwakin mutum 29, sannan aka ceto mutum 50, yayin da mutum biyu suka ɓace.
Sai dai daga baya, shugaban Ƙaramar Hukumar Borgu, Abdullahi Baba Ara, ya tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasu ya ƙaru zuwa 60,
Hakazalika, ya ce ƙarin wasu mutum 10 na cikin mawuyacin hali, yayin da har yanzu ake neman wasu.
Dagacin yankin Shagunu, Sa’adu Inuwa Muhammad, ya ce ya je wajen bayan aukuwar hatsarin, inda ya tabbatar da cewa jirgin ya ɗauki mutane sama da 100, waɗanda mafi yawansu mata da yara ne.
Ya ce an gano gawarwakin mutum 31, kuma an binne huɗu daga cikinsu a ranar Talata.
A halin yanzu dai, ana ci gaba da ƙoƙarin gano waɗanda suka ɓace.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link