Shugabanni marasa shiri ne matsalar Afirka — Obasanjo

[ad_1]



Tsohon Shugaban ƙasar Nijeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa rashin shugabanci na gari shi ne babban abin da ke kawo cikas ga ci gaban ƙasashen Afirka.

Obasanjo ya bayyana cewa, idan aka samu shugabanni marasa inganci, ƙasashe kan rarrabu, ana sace dukiyar ƙasa, yara marasa ilimi sukan kwana da yunwa, sannan matasa masu kyakkyawar makoma sukan yanke ƙauna tare da ɗaukar “mummunan fargaba” wajen neman abinci a ƙasashen waje.

Obasanjo ya bayyana  hakan ne ranar Alhamis a birnin Abeokuta, Jihar Ogun, yayin da yake jawabi ga ɗaliban da suka kammala karatu a Cibiyar Shugabanci ta Olusegun Obasanjo (OOLI).

An gudanar da taron yaye ɗaliban ne yayin taron bitar taya tsohon shugaban ƙasar murnar cikarsa shekaru 89 da haihuwa, mai taken “Wayar da kan Afirka na Duniya: Daga wani mataki  zuwa Farfaɗowa.”

Taron, wanda aka gudanar a Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta, ya samu halartar manyan mutane, da suka hada da tsofaffin ‘yan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyun LP,  Peter Obi da na NNPP,Rabiu Kwankwaso; Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun; da tsoffin gwamnonin jihar, Sanata Ibikunle Amosun da Otunba Gbenga Daniel.

A cewar Obasanjo, ya kafa wannan cibiya ne saboda bayan shekaru hamsin da ya kwashe yana hidimar ƙasa, ya fahimci cewa babban abin da ya fi yi wa Afirka ƙaranci ba kudi ba ne, ba fili ba ne, kuma ba fasaha ba ne, face shugabanci.

Yayin da yake bayyana rashin shugabanci a matsayin masifar da ke dakushe ci gaban Afirka, ya ce, “Na ga abin da shugaba guda ɗaya mai inganci zai iya aikatawa.”


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *