NPA Ta Baje Kolinta A Taron Zuba Jari Na Kasa Da Kasa Na Inbestopia
[ad_1]
Nijeriya ta karbar bakunci babban taron na kasa da kasa na masu zuba jari a fannin sufuri, inda Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Kasa NPA, ta zayyano wasu manyan manufofi, domin kara samar da intantattun kayan aiki, ga Tashoshin Jiragen Ruwa na kasar.
Taron wanda zai guna a jihar Legas, ya samu halartar jiga-jigan masu zuba jari a fannin sufurin Jiragen Ruwa daga ketare.
- Rikicin Iran Da Amurka: Gabas Ta Tsakiya Ta Ɗauki Zafi
- Dabara Ta Rage Ga Mai Shiga Rijiya
Za a gudanar da taron ne, a tsakanin Nijeriya da kuma Daular Larabawa wato UAE.
Taron wanda ya gudanar a ranar 2 na watan Fabirairun 2026, ya gudana ne, a cibiyar Eko, da ke a Legas, ya samu halartar manyan jami’ian gwamnati da masu zuba jari daga ketare da jagororin manyan masana’antu, inda suka yi tattaunawa mai zurfi, kan yadda za a amafa da albakatun, da ke a yankin.
Kazalika, tattaunawar, ta shafi yadda za a samar da manyan kayan aiki da samar da makamashi da samar da tsarin kudade, wadanda sune, suka kasance, kan gaba, wajen bunkasa tattalin arzkin Afirka, na dogon zango.
A cikin sanarwar da Janar Manja na sashen hulda da jama’a a NPA, Ikechukwu Onyemekara, NPA ta ce, halartar masu zuba jarin taron, ya nuna irin mayar da hankali da Nijeriya ta yi, wajen kara saita fannin na sufurin Jiragen Ruwan kasar, musamman domin bayar da damar, ci gaba da gudanar da hada-hadar kasuwanci da kuma kara karfafa hukdar kasuwanci, a tsakanin kasashen da ke a Afirka.
A cewar NPA, taron na Inbestopia Lagas, an gudanar da shi ne, sabada nuna ra’ayin kara bunkasa fannin, da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi.
Sanawar ta kara da cewa, taron ya biyo bayan wata ziyara da Nijeriya ta kai UAE ne, a watan Janairun 2026, bayan taron kasa da kasa na mako, da aka gudanar a Abu Dhabi.
Kazalaika, a lokacin ziyarar a Abu Dhabi, Nijeriya da UAE, sun rattaba hannun yarjejeniya ta hadakar bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu, wato CEPA.
Babban abin da ake son cimma buri, shi ne, kara karfafa hadaka wajen kaara samar da makamashi da kayan aiki da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci, ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.
Bugu da kari, shugaba Tinubu, ya sanar da dalilin da ya sa, Nijeriya, za ta karbi bakuncin taron na Inbestopia da za a gudanar a Legas, musamman bisa nufin janyo hanlakin masu zuba jari daga ketare.
Hakazalika, Shugaban Hukumar ta NPA Dakta Abubakar Dantsoho da kuma Mohamed Almenhali, Babban Jami’I a Tashoshin Jiragen Ruwa na Abu Dhabi, sun kasance Alkalai wajen taron, inda suma suka gabatar da kasida mai taken, “ Samar Da Ingantattun Kayan Aiki a Tashoshin Jiragen Ruwa domin kara bunkasa hada-hadar kasuwanci, a mataki na gaba.
Alkalancin taron, ya kuma mayar da hankali wajen yadda za a kara karfafa samar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwa da zamanantar da hada-hadar kasuwanci ta hanyar yin amfani da fasahar zamani.
Kasashen biyu, za su kuma amfana da juna a bangaren zuba jari, tare da saita kasuwancin a Afirka ta Yamma, wanda hakan, zai kara habaka hada-hadar kasuwanci.
Masu jawabi da ban da ban, sun gabatar da kasidu, wadanda suka hada da, Babban Shugaba na Inbestopia, Dakta Jean Fares da ministar ma’aikatar bunkasa kasuwanci da zuba jari, Dakta Jumoke Oduwole da ministan ma’aiktar zuba jari na UAE Mohamed H. Alsuwaidi.
Sauran sun hada da; kasidun Babban Jami’I kuma Manajin Darkta na FIRST da Ademola Adeyemi-Bero shugaba kuma Babban jami’I na AFC, Samaila Zubairu da sauransu.
Kazalika, Hukumar ta NPA, ta himmatu wajen kara fadada sauye-sauyen ci gaban fannin da kara bunkasa ayyukanta, musamman domin a cimma nasara, kan manufofin kara ciyar da ayyukan hukumar gaba.
A cewar hukumar hadakar da ta yi da UAE wanda hakan ya kuma haifar da taron na Inbestopia, kwalliya ta biya kudin Sabulu, musamman duba da cewa, hakan ya kara samar da damar zuba jari, wanda hakan zai kuma samar da sakamako mai kyau na tattaunawar da shugaba President Tinubu, ya yi a kwanan baya da UAE.
[ad_2]
Source link