An Kammala Aikin Samar Da Wutar Lantarki Ta Iska Da Kamfanin Sin Ya Gina A Habasha
An yi bikin kammala aikin samar da wutar lantarki ta iska na Aysha II na Habasha wanda kamfanin Sin ya gudanar da kwangilar ginawa kwanan nan a jihar Somali dake gabashin kasar, inda firaministan Habasha Abiy Ahmed, shugaban Djibouti Ismail Omar Guelleh, da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud suka halarta.
Mr. Abiy a wurin taron ya bayyana cewa, makamashi mai tsabta yana da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin Habasha cikin dogon lokaci, kuma aikin samar da wutar lantarki ta iska na Aysha II ya nuna kokarin Habasha na cin gashin kanta ta hanyar amfani da albarkatun cikin gida. Ya ce, “Na gode wa kamfanin wutar lantarki na Habasha, da kamfanin Sin na Dongfang mai kera na’urorin wutar lantarki da ya yi kwangilar aikin, da kuma al’ummar yankin, na gode muku don gudunmawar da kuka bayar don kammala matakin farko na aikin.”
Bisa ga abin da aka sani, an fara gina aikin samar da wutar lantarki ta iska na Aysha II a shekara ta 2017, inda kamfanin Sin na Dongfang mai kera na’urorin wutar lantarki ya rattaba hannu kan kwangilar tare da kamfanin wutar lantarki na Habasha. Yawan wutar lantarki da aikin zai samar da aka tanada zai kai megawatts 120, tare da hada na’urorin samar da wutar lantarki ta iska guda 48, kowannensu yana da karfin samar da megawatts 2.5. A halin yanzu, an kammala hada na’urorin guda 32 na matakin farko, kuma sun fara samar da wutar lantarki kamar yadda ake fata. (Amina Xu)