He Lifeng: Muna Maraba Da Kamfanonin Amurka Su Yi Amfani Da Damammakin Ci Gaban Kasar Sin Tare Da Zurfafa Hadin Gwiwa

[ad_1]

Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar majalisar kula da cinikayyar Amurka da Sin a nan birnin Beijing, da yammacin yau Lahadi 22 ga wata.

He Lifeng ya ce, dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka ita ce dangantakar kasashe biyu mafi muhimmanci a duk fadin duniya a yau. Ya yi fatan cewa, majalisar kula da cinikayyar Amurka da Sin za ta ci gaba da taka rawa a matsayin gada da hanyar sada zumunta, da sa-kaimi ga mu’amalar abokantaka, da samar da kwanciyar hankali da inganci a fannin ci gaban tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.

Ya yi fatan kamfanonin Amurka za su yi cikakken amfani da damammakin ci gaban kasar Sin, da kyakkyawan cin gajiyar kasuwar kasar Sin, da kara samar da kwanciyar hankali da kuzari mai kyau ga dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka.

A nasu bangaren, shugaban kwamitin amintattu na majalisar kula da cinikayyar Amurka da Sin Raj Subramaniam, da kuma shugaban majalisar Sean Stein, sun bayyana cewa, ‘yan kasuwan Amurka suna da kyakkyawan fata game da makomar bunkasar kasar Sin, kuma suna son ci gaba da zurfafa nazari kan kasuwar kasar Sin, da taka rawar gani, da ci gaba da inganta zurfafa hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *