Ta’addanci: An fi kashe Musulmi a kan Kiristoci a Najeriya — Jakadan Amurka

[ad_1]



Jakadan Amurka na Musamman kan Harkokin Larabawa da Afirka, Massad Boulos, ya ƙaryata iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya babu gaira babu dalili.

Ya ce hare-haren ta’addanci da ke faruwa a ƙasar suna shafar Kiristoci da Musulmai baki ɗaya.

Boulos, wanda mashawarci ne ga Shugaban Amurka Donald Trump, ya faɗi hakan ne bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a ranar Jumma’a.

Wasu ’yan majalisar dokokin Amurka sun nemi gwamnatin Amurka ta sanya Najeriya cikin jerin ƙasashe masu hatsari wadda ake zaluntar Kiristoci.

Sai dai Jakadan ya ce lamarin ba haka yake ba.

“Waɗanda suka san Najeriya sosai sun fahimci cewa ta’addanci ba shi da launi, addini, ko ƙabila,” in ji Boulos.

“Kungiyoyin Boko Haram da ISIS sun kashe Musulmai sama da Kiristoci. Mutane daga kowane ɓangare na fama da wannan tashin hankali. Ba a iya wani ake kai wa hari ba.”

Ya bayyana cewa rikicin da ake samu a Arewa ta Tsakiya a Najeriya, rikici ne tsakanin manoma da makiyaya, wani lokaci yana shafar Kiristoci, amma asalin rikicin yana da nasaba da harkar noma, ba addini ba.

“Ba shi da nasaba da addini,” in ji shi.

“Najeriya ƙasa ce da ta ƙunshi ƙabilu da addinai da dama waɗanda suke zaune tare tsawon shekaru. Bai kamata a juya wannan matsala zuwa ta koma ta addini ba.”

Boulos, ya kuma yaba wa gwamnatin Shugaba Tinubu bisa ƙoƙarin da ta ke yi wajen inganta tsaro, inda ya ce sakamakon ƙoƙarin ya fara bayyana.

Maganar “kisan gillar Kiristoci” a Najeriya ta ƙara yawaita ne bayan jawabin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA).

A yayin taron ya yi kira da a samar da zaman lafiya a Gaza da kuma goyon bayan tsarin ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Falasɗinu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *