Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL
[ad_1]
Hukumar gasar firimiya ta Nijeriya (NPFL) ta ƙaƙabawa Katsina United tara mai tsanani bayan samun ta da laifin gazawa wajen samar da tsaro a wasan da ta kara da Barau FC a filin wasa na Muhammad Dikko dake Katsina a ranar Asabar. Wannan hukunci na zuwa ne bayan makonni kaɗan da irin wannan aka kakabawa Kano Pillars saboda rashin ɗa’a da saɓa doka a gasar.
Rahotanni sun nuna cewa rikici ya ɓarke a filin wasan bayan Barau FC ta farke ƙwallo, inda wasu magoya bayan Katsina United suka kutsa cikin fili, lamarin da ya janyo mummunan rauni ga ɗan wasan Barau, Abraham, a wuyansa. Wannan ya jawo tayar da tarzoma da ta jefa ƴan wasan cikin ruɗani.
A cewar sanarwar NPFL, an ci tarar Katsina United Naira miliyan ɗaya bisa laifuka uku: jefa abubuwa cikin fili, rashin tsawatarwa magoya baya, da haddasa hargitsi a wasa. Haka kuma, ƙungiyar za ta biya Naira miliyan biyu saboda gazawa wajen samar da isasshen tsaro, tare da ɗaukar nauyin gyaran motocin Barau FC da aka lalata.
Jimillar tarar da Katsina United za ta biya ta kai Naira miliyan tara (₦9m), tare da umarni daga NPFL cewa duk sauran wasanninta na gida a kakar bana za ta buga su a garin Jos, jihar Filato. Hukumar ta kuma bai wa ƙungiyar awa 48 ta ɗaukaka ƙara idan bata gamsu da hukuncin ba.
[ad_2]
Source link