Rikicin Jos: Tinubu Ya Jinkirta Tafiyarsa Zuwa Ogun, Zai Kai Ziyara Filato
[ad_1]
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jinkirta tafiyarsa da ya shirya zuwa Iperu a Jihar Ogun, inda zai ƙaddamar da fara aikin filin jirgin jigilar kaya.
A maimakon haka, zai tafi Jos, babban birnin Jihar Filato, domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar kan hare-haren da aka kai wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
- Adadin Lambar Shaidar Mallakar Kira Dake Hannun Kamfanoni Ya Kai Kaso 54% Na Jimillarsu A Sin
- Farfadowar Halittun Ruwa A Kogin Yangtze Ta Nuna Kyakkyawan Yanayi
A cewar mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, daga nan shugaban zai wuce Legas domin yin hutu.
A ranar Asabar, 4 ga watan Afrilu, Tinubu zai je Ogun domin ƙaddamar da filin jirgin jigilar kaya da kuma fara amfani da jiragen sama guda biyu da za su taimaka wajen shigo da kayayyaki da fitar da su, domin bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Haka kuma zai ƙaddamar da sabon ginin ofishin Federal Operations Unit na Hukumar Kwastam ta Nijeriya da motocinta.
Bayan haka, zai koma Legas domin ci gaba da hutu, inda kuma ake sa ran zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin Gwamna Babajide Sanwo-Olu ta aiwatar, ciki har da gadar Ojota/Opebi Link.
Kafin ya dawo Abuja, shugaban ƙasar zai ziyarci Bayelsa a ranar 10 ga watan Afrilu domin ƙaddamar da wasu ayyuka da Gwamna Duoye Diri ya kammala.
[ad_2]
Source link