’Yan bindinga sun yi garkuwa da dalibai 25 a Kebbi
[ad_1]
’Yan ta’adda sun harbe Mataimakin Firinsifal har lahira, sa’annan suka yi garkuwa da dalibai 25 a Makarantar ’Yan Mata ta Gwamnati (GGCSS) da ke yankin Maga a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun bindige Malam Hassan Yakubu Makuku ne a yayin da yake kokarin kare daliban, a lokacin farmakin da aka kai makarantar da misalin karfe 5.20 na Asubahin ranar Litinin.
Wani shaida ya ce, “Harin ya dimauta al’ummar garin Maga, yanzu muna cikin zullumi da alhini.” Ya kara da cewa, ’yan ta’addan sun harbe Malam Hassan ne a yayin da yake kokarin hana su tafiya da daliban.”
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link