PRP za ta gyara Najeriya idan aka zaɓe ta — Baba-Ahmed

[ad_1]



Sabon shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa jam’iyyar ce kaɗai za ta iya magance matsalolin da ke addabar Najeriya idan har ta samu nasara a zaɓen shekarar 2027.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron rantsar da sabbin shugabannin jam’iyyar da aka gudanar a Abuja.

Baba-Ahmed, ya jaddada cewa PRP jam’iyya ce mai haɗin kai wadda ba ta fama da rikici.

Ya ƙara da cewa har yanzu jam’iyyar tana da yaƙinin cewa Najeriya za ta gyaru, kuma ta shirya samar da mafita ga dukkanin ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.

Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su dawo cikin jam’iyyar tare da yin rajistar zaɓe, yana mai nuni da cewa PRP ita ce mafi dacewa a halin yanzu, musamman ganin yadda ta gudanar da babban taronta na ƙasa cikin gaskiya da adalci.

A cewarsa, tambarin jam’iyyar wato “Makulli”, yana nufin buɗe ƙofofin samar da shugabanci na gari da kuma fitar da ’yan Najeriya daga ƙangin talauci.

Shugaban ya jinjina wa mambobin jam’iyyar bisa jajircewarsu duk da ƙalubalen da suka fuskanta na tsawon lokaci, yana mai cewa sun zaɓi tafarkin gaskiya maimakon biye wa son zuciya.

Haka kuma, ya yi alƙawarin samar da jagoranci mai cike da gaskiya da riƙon amana, tare da bayyana cewa ya fahimci nauyin amanar da aka ɗora masa.

Baba-Ahmed, ya bayyana cewa manyan abubuwan da jam’iyyar za ta fi mayar da hankali a kansu sun haɗa da: inganta tsaro, samar da shugabanni na gari, da kuma tabbatar da gudanar da zaɓe na gaskiya.

Daga ƙarshe, ya buƙaci ’yan Najeriya da su daina bin ’yan siyasa saboda abubuwan da suke bayarwa, maimakon haka su yi tunanin makomar ƙasar tare da haɗa kai domin gina Najeriya.

Ya jaddada cewa PRP a shirye take ta lashe zaɓe tare da kawo sauyi na zahiri.

A wajen taron, tsohon shugaban jam’iyyar, Falalu Bello, ya miƙa ragamar mulki tare da wasu muhimman takardu da tambarin jam’iyya da kuma kundin tsarin mulki ga sabbin shugabannin.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *