Masana’antun Fasahohin Zamani Na Sin Sun Samu Habaka A Sulusin Farko Na Bana

[ad_1]

Sabbin bayanan haraji sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin na ci gaba da tafiya cikin daidaito, bisa karfafuwar kirkire-kirkire, kamar yadda aka samu shaidar hakan a fili daga habaka mai gwabi da aka samu a kudaden shiga na masana’antun manyan fasahohi a sulusin farko na shekarar 2026.

Bayanan da hukumar kula da haraji ta kasa ta fitar a yau Laraba sun nuna cewa, kudaden shiga da aka samu daga cinikin sayar da kaya na masana’antun manyan fasahohi daga ranar 1 ga Janairu zuwa 25 ga Maris, sun karu da kashi 14.6 idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Masana’antun kera kayayyaki na manyan fasahohi da sauran ayyuka da suka jibanci hakan kuma, sun samu karuwar kudin shiga da kashi 12.7 da kuma kashi 15.8 bi-da-bi.

Bayanan sun kuma nuna cewa, sakamakon bukatar da ake da ita a kan fasahar kirkirarriyar basira ta AI da kuma cibiyoyin karfafa sarrafa bayanai da inganta saurin aikin na’urori, kudaden shiga da aka samu daga cinikin sayar da zayyanar kwakwalwan na’urorin kwamfuta su ma sun karu sosai. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *