ICPC za ta gurfanar da El-Rufai bayan kwana 35 a tsare

[ad_1]



Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ICPC ta sanar da cewa za ta gurfanar da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a gaban kotu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

Hukumar ta ce za a gurfanar da El-Rufai tare da wasu da ake zargi abokan hulɗarsa ne a kotuna daban-daban da ke Jihar Kaduna, bisa tuhume-tuhume da suka haɗa da zamba, wulaƙanta madafan iko, da kuma almundahanar kuɗi.

Rahotanni sun nuna cewa za a gurfanar da shi ne bayan kwanaki 35 ana tsare da shi ba tare da an kai shi kotu ko an tuhume shi a hukumance ba, lamarin da ya jawo suka daga lauyoyi da kuma kafafen yaɗa labarai.

A makon da ya gabata ne wasu lauyoyi suka soki ci gaba da tsare tsohon gwamnan ba tare da an gurfanar da shi ba, suna cewa hakan ya saɓa wa dokokin ƙasa.

Da yake jawabi kan batun, kakakin ICPC, John Odey, ya bayyana cewa hukumar ta shigar da ƙarar ne tun ranar 18 ga Maris, 2026.

Ya ce za a gurfanar da El-Rufai da wani Joel Adoga a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna a ranar Talata, 24 ga Maris, 2026.

A cewarsa, tuhume-tuhumen sun haɗa da mallakar kadarorin gwamnati ba bisa ƙa’ida ba da kuma halasta kuɗaɗe haramun.

Kazalika, Odey ya ce an kuma shigar da wata ƙara daban a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna, inda ake tuhumar El-Rufai da wani Amadu Sule da laifuffuka da suka haɗa da cin zarafin madafan iko, zamba da kuma bai wa wasu gata ba bisa ƙa’ida ba.

Sai dai ya ƙara da cewa ranar da za a gurfanar da su a kotun jihar za a sanar da ita daga baya, gwargwadon yadda kotu ta tsara.

Odey ya jaddada cewa an riga an miƙa wa El-Rufai takardun tuhuma, tare da cewa ICPC za ta ci gaba da bin doka da oda a duk matakan shari’ar.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *