Gwamna Inuwa ya naɗa sabbin shugabanni a ma’aikatar lafiya ta Gombe
[ad_1]
Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da naɗa sabbin shugabanni biyu a Ma’aikatar Lafiya ta Jihar.
An naɗa Dokta Lawan Bala a matsayin Babban Sakataren Ma’aikatar Lafiya, sannan Dokta Mohammed Bello Abdulkadir a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci ta Jihar Gombe.
Kafin wannan lokaci, Dokta Lawan Bala shi ne Babban Sakataren Hukumar Kula da Asibitoci, inda ya taka muhimmiyar rawa wajen inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.
Shugaban Ma’aikata na Jihar Gombe, Alhaji Ahmed Kasimu Abdullahi ne, ya bayyana amincewar gwamnan.
Ya ce wannan mataki yana cikin shirin gwamnati na ƙara inganta harkokin lafiya bayan nasarar taron ƙoli kan lafiya na farko da aka gudanar a jihar.
A wata sanarwa da Kakakin Gwamna, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, ya ce Gwamnan ya amince da aiwatar da tsarin albashi na CONMESS da CONHESS ga ma’aikatan lafiya, tare da yin wasu gyare-gyare domin inganta shugabanci a wannan ɓangare.
Dokta Mohammed Bello Abdulkadir, wanda kafin yanzu shi ne Daraktan Harkokin Lafiya a Ma’aikatar Lafiya, ya kasance ƙwararre a aikin likitanci da gudanar da manufofin kiwon lafiya.
Ana sa ran sabbin shugabannin za su ci gaba a harkokin lafiya a jihar.
Gwamna Inuwa, ya bayyana cewa yana da cikakken tabbaci cewa za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen inganta kiwon lafiya a Jihar Gombe.
Naɗin nasu ya fara aiki nan take.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link