NSCDC Ta Kama Mutane 3 Kan Kisan Jami’inta A Kano
Rundunar tsaron farar kaya (NSCDC) reshen Jihar Kano ta kama wasu mutane uku ɗauke da makamai, bisa zargin hannu a kisan wani jami’inta, AbduRauf A. Shariff, yayin da yake ƙoƙarin daƙile aiyukan ɓata-gari a cikin birnin Kano.
Kakakin rundunar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya bayyana cewa marigayin na bakin aiki ne a yankin Court Road, lokacin da ya ci karo da wasu mutane da ake zargin suna satar wayoyi da aikata laifuka, inda ya yi yunƙurin dakatar da su.
- Ministan Wajen Sin Ya Zanta Da Takwaransa Na Koriya Ta Kudu Ta Wayar Tarho
- De Bruyne Ya Kammala Komawa Napoli Bayan Barin Man City
Ya ce a yayin ƙoƙarin cafke su, waɗanda ake zargin sun kai masa hari da makamai, lamarin da ya jikkata shi matuka, wanda daga bisani ya yi sanadin mutuwarsa. Daga nan ne jami’an NSCDC suka iso wurin tare da cafke mutum uku daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere.
Abdullahi ya ƙara da cewa waɗanda aka kama suna tsare a hannun hukuma, yayin da ake ci gaba da bincike tare da haɗin gwuiwar Rundunar Ƴansandan domin kamo sauran da suka tsere. Ya kuma bayyana cewa an kai gawar marigayin duba lafiyar likita kafin a tabbatar da rasuwarsa.
Rundunar NSCDC ta jaddada cewa ba za ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen tabbatar da cewa duk waɗanda ke da hannu a wannan aika-aika an hukunta su bisa doka, tare da tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a Kano.