’Yan bindiga sun kashe mutum 30 a wani sabon hari a Zamfara

[ad_1]



’Yan bindiga sun kai hari ƙauyen Dutsin Dan Ajiya da ke Ƙaramar Hukumar Anka, inda suka kashe sama da mutum 30 tare da sace wasu da dama.

Harın ya faru ne a daren ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairu 2026 da misalin ƙarfe 12 na dare.

Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan gwamnatin jihar ta ƙaddamar da sabbin kayan tsaro da jirage marasa matuƙa domin yaƙi da matsalar tsaro.

Rahotanni daga mazauna ƙauyen sun ce maharan sun zo ne a kan babura, inda suka tare hanyoyin shiga ƙauyen sannan suka riƙa harbe-harbe.

Aminiya ta ruwaito cewa harin ya biyo bayan wani hari daban da wasu mahara suka kai Ƙaramar Hukumar Arewa, inda suka kashe mutum 33.

Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Yazid Abubakar, bai yi nasara ba zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *