’Yan bindiga sun kai hari a Kankia
[ad_1]
Dandazon ’yan bindiga sun kai hari a yankin Kankia da ke Jihar Katsina inda suka halaka mutum daya tare da jikkata wasu da dama.
Shaidu sun ce ’yan bindiga kimanin 100 a kan babura ne suka kai harin a yankin Kwadawa da ke Gundumar Gashi da ke Karamar Hukumar Kankia, inda ake Ana zargin maharan sun kai harin daukar fansa ne,
Maharan da suka kai farmaki a yankin da ke Gabahsin karamar hukumar, sun sace dabbobi da ba a san adadinsu ba, suna masu barazanar halaka duk mutanen yankin.
Wakilinmu ya ruwaito cewa a halin yanzu mazauna yankunan Bogga, Taiba Badole, Arahiya, Kwandawa, Rumawa, Gangara da Rugar Bindo da ke gundumar Gachi da kuma Fakuwa/Kafindangi suna yin kaura domin tsira da rayuwarsu.
Wani ganau ya ce’yan bindigar suna kutsawa zuwa yankunan da a baya suke zauna cikin aminci, kmar Kankia , Charanchi, Kusada da a baya ba sa fama da matsalar tsaro.
Kazalika mazauna kauyukan Tama da Dokaji da ke Karamar Hukumar Bindawa sun bayyana fargabarsu da bayan samun labarin harin na Kankia, mai makwabtaka da su.
Haladu Badole ya ce, “Kimanin kwanaki uku ke nan da muka lura da wasy bakin fuska a yankunanmu, kuma a daren jiya sun kai hari suka sace dabbobin mutane.”
Mazauna yankin sun yi kira ga hukumomi da su gaggauta tura jami’an tsaro zuwa yankin domin samar da tsaro.
A baya yankin Gabashin Karamar Hukumar Kankia ya kasance cikin amici duk da ’yan hare-haren da aka samu a yankunan Rimaye, Magam, Sukuntuni, Gyaza daKunduru da ke karamar hukumar.
Wakilinmu ya tuntubi kakakin ’yan sandan jihar, amma ya bayyana masa cewa suna gudanar da bincike domin gano hakikanin halin da ake ciki.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link