An kama mai POS kan damfarar wata mata Naira dubu 375 a Kuros Riba
[ad_1]
Rundunar ’yan sandan Jihar Kuros Riba ta kama wani matashi mai shekara 24 da haihuwa, mai suna Divine Joseph, bisa zargin damfarar kuɗi ta hanyar na’urar cire kuɗi ta zamani (POS).
A cewar bayanan da Aminiya ta samu, wanda ake zargin ya damfari wata mai sayar da jaridu da mujallu, wadda ta zo wurinsa domin cire kuɗi.
Bayanai sun ce Divine Joseph ya ƙyallara ido a yayin da matar ke shigar da lambobin sirrin katinta na ATM, inda daga bisani ya karkatar da kuɗinta zuwa nasa asusu ba tare da ta sani ba.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, bayan ya sallami matar ta ta tafi, sai ya ci gaba da cire mata kuɗi a hankali har adadin kuɗin da ya ya kai Naira 375,000.
Matar ta gano abin da ya faru ne bayan ta fara samun saƙonnin cire kuɗi a wayarta wanda ta riƙa mamaki da sanin cewa ba ita fitar da kuɗin ba, lamarin da ya sa ta kai ƙorafi ofishin ’yan sanda na Uwanse, da ke ƙaramar hukumar Kalaba ta Kudu.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Sunday Eitokpa, ya tabbatar wa wakilinmu faruwar lamarin, inda ya ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya yaudari matar ne ya sa ta shigar da lambobin katinta da kuma na shaidar ɗan ƙasa.
ASP Eitokpa ya ce Divine Joseph ya amsa laifin, inda ya bayyana cewa tun farko matar ta zo wurinsa ne domin cire Naira 1,400, amma ya canja adadin kuɗin zuwa Naira 77,000 ba tare da ta sani ba, yana cire mata kuɗi a duk lokacin da ta zo wurinsa, ganin cewa tana da kuɗi masu yawa a asusunta.
’Yan sanda sun ce wanda ake zargin ya yi amfani da katin cire kuɗi na bogi wajen kutsawa cikin asusun matar bayan ya yaudare ta ta shigar da lambobinta na sirri.
Rundunar ta ce ana ci gaba da tsare matashin domin zurfafa bincike, kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da shi a gaban kotu.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link