Sakamakon Matsin Lambar Jami’an Tsaro, ‘Yan Ta’adda Na Fuskantar Ƙarancin Abinci
[ad_1]
Wani rahoto daga jihohin Neja da Zamfara, ya nuna cewa ɓullar cututtuka a tsakanin ƴan ta’adda na ƙara yin tasiri kan ayyukansu, musamman hare-hare da satar jama’a, sakamakon ƙarancin kuɗi, kayan abinci da magunguna a maɓoyarsu. Kamar Yadda wani da ya kuɓuta daga hannun ƴan fashin dajin wanda ya shafe sama da kwanaki 40 a hannunsu ya shaida wa manema labarai a Kano
Majiyoyi sun bayyana cewa halin da suke ciki na rashin wadatattun kayayyakin buƙata ya sa suke fuskantar matsin lamba, lamarin da ya rage musu ƙarfin guiwa a wasu yankuna.
Wani mutum da ya kuɓuta daga hannun mahara a Jihar Neja ɗan asalin Jihar Kano wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana irin halin rashin lafiyar da ya tarar a sansanin da aka tsare shi. A cewarsa, ba waɗanda aka yi garkuwa da su kaɗai ba ne ke fama da cututtuka, hatta wasu daga cikin maharan na cikin irin wannan hali.
- Shalƙwatar Tsaro Ta Ƙasa Na Shirin Gyaran Tsarin Tubabbun Ƴan Ta’adda
- Direbobi Sun Koka Kan Dawowar Matsalar Tsaro Kan Babbar Hanyar Damaturu Zuwa Biu
Ya ce ya shafe kwanaki cikin tsananin fargaba da tsoro, yana gudun kamuwa da cutar da ke addabarsu, duba da yadda ba su da magunguna ko kulawar lafiya a cikin dajin.
Sai dai ya ƙara da cewa idan jami’an tsaro za su ƙara ƙaimi a wannan lokaci, akwai yiwuwar a murƙushe tasirin ƴan ta’addan, la’akari da irin mawuyacin halin da suke ciki a halin yanzu.
Daga ƙarshe, ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara zage dantse wajen kawar da matsalar ƴan bindiga a yankunan da abin ya shafa, yana mai jaddada cewa haɗin kan jami’an tsaro da al’umma, tare da addu’o’in jama’a, na da muhimmiyar rawa wajen kawo ƙarshen matsalar.
[ad_2]
Source link