Ista: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Juma’a Da Litinin A Matsayin Ranakun Hutu

[ad_1]

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Juma’a, 3 ga Afrilu, da kuma Litinin, 6 ga Afrilu, 2026, a matsayin ranakun hutu na ƙasa domin bikin Ista na wannan shekara.

A cewar wata sanarwa da Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya fitar a ranar Laraba, ranakun hutun su ne ‘Good Friday’ da kuma ‘Easter Monday’.

  • Yadda Jigo A APC Na Kano Ya Rasu A Otal A Abuja
  • Bahallatsar Gabas Ta Tsakiya: Sin Da Pakistan Sun Ba Da Mafita

Ministan ya kuma taya daukacin Kiristoci murna a Nijeriya da ma waɗanda ke zaune a ƙasashen waje.

Tunji-Ojo ya bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi kyawawan halaye da ke tattare da wannan lokaci, inda ya ce, “Ina taya dukkan Kiristoci a Nijeriya da kuma na ƙasashen waje murnar bikin Easter. Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su rungumi halayen sadaukarwa, yafiya, juriya, da soyayya, kamar yadda rayuwa da koyarwar Yesu Almasihu suka nuna.”

Ya kuma yi kira da a ƙarfafa haɗin kai tsakanin al’umma, yana mai jaddada muhimmancin zaman lafiya tare da juna.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *