’Yan bindiga sun mamaye mazaɓata —Ɗan majalisar Katsina
[ad_1]
A yayin zaman majalisar dokokin jihar Katsina, Babban Mai Tsawatarwa na majalisar, Hon. Ibrahim Umar Dikko, ya fashe da kuka a gaban takwarorinsa, yana bayyana yadda ’yan bindiga suka mamaye mafi yawan yankunan da ke cikin Ƙaramar Hukumar Matazu da yake wakilta.
Hon. Dikko ya bayyana cewa daga cikin gundumomi 10 da ke cikin Matazu, guda 8 sun faɗa hannun ’yan bindiga, inda ya ce manoma ba sa iya zuwa gonakinsu saboda tsoron harin da ake kai musu.
“A jiya da safe, a bakin garin kusa da makarantar sakandare, sun kashe wani matashi sannan suka sace shanu hudu da ake amfani da su wajen noma,” in ji shi cikin hawaye.
Ya kara da cewa a cikin kwanaki biyu da suka gabata, akalla manoma 12 aka kashe a gonakinsu.
“A jiya sun kashe manoma biyar a gonarsu. A ranar da ta gabata kuma sun kashe manoma bakwai. Wallahi, ba za a iya zuwa gona ba. Muna cikin mawuyacin hali, muna bukatar taimako,” in ji shi cikin murya mai sosa rai.
Wannan kukan da ɗan majalisar ya yi ya ƙara jaddada irin halin kunci da al’ummomin jihar Katsina ke ciki, musamman a yankunan da ke fama da hare-haren ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.
An sace soja an kai hari a ƙauyuka 10 a Sakkwato
A wani lamari makamancin haka, rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun mutu, ciki har da jami’ai hudu na hukumar tsaron al’umma na jihar, yayin da wasu da dama aka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.
Harin da ake zargin wani shahararren shugaban ’yan bindiga mai suna Kallamu ya jagoranta — wanda ke da alaka da Bello Turji — ya shafi akalla kauyuka 10 daga ranar Laraba zuwa Asabar da ta gabata.
Kauyuƙan da aka kai wa hari sun hada da: Ɗan Tudu, Lafinge, Gidan Bature, Makuwana, Turtsawa, Garki, Faru, Najingi, da Zannan Bango.
“Sun kashe mutane da dama, sun sace wasu, sun kwashe fiye da shanu 100, sannan sun tare hanyar Yankasuwa zuwa Masawa inda suka sace matafiya,” in ji wani mazaunin yankin.
Galadiman Gobir, Alhaji Abubakar Sulaiman, ya tabbatar da mutuwar mutane 8 a kauyukan Dan Tudu da Makuwana, tare da sace mutane 50 a kauyuka daban-daban.
“Sun kai hari har sansanin sojoji a Dan Tudu, inda suka kashe soja daya da jami’an tsaro hudu. Har yanzu ba a tantance adadin wadanda aka sace ba,” in ji shi.
Wasu mazauna yankin sun ce an kai hare-hare sau biyu ko uku a wasu kauyuka cikin kwanaki hudu, lamarin da ya tilasta wa jama’a barin gidajensu.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, Ahmed Musa, ya tabbatar da harin da aka kai Makuwana da Gidan Bature, inda ya ce ya ziyarci Sabon Birni da Goronyo domin tantance lamarin da kuma jajanta wa iyalan da abin ya shafa.
Mai dangantaka
[ad_2]
Source link