Sojoji sun daƙile harin ’yan ya’adda a Yobe
[ad_1]
Dakarun haɗin gwiwa na Operation Haɗin Kai sun yi nasarar daƙile wani hari da ake zargin mayaƙan Boko Haram da na ISWAP suka kai a Jihar Yobe.
Wannan ƙazamin artabu ya auku ne a daren ranar 30 ga watan Maris, da misalin ƙarfe 10:05 na dare, lokacin da maharan suka ƙaddamar da hari kan sansanin sojoji (Forward Operating Base) da ke Bukarti a Ƙaramar Hukumar Yunusari.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa dakarun sojin sun yi bajinta, inda suka yi gaggawar mayar da martani, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan tserewa.
A yayin arangamar, soja guda ɗaya ya samu rauni, inda aka garzaya da shi asibiti kuma a halin yanzu yana cikin yanayi mai kyau.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi nasarar tserewa da wasu kayan aiki kafin dakarun su fatattake su.
Kayan sun haɗa da motar yaƙi ƙirar gun truck mai ɗauke da bindiga, motar Civilian JTF guda ɗaya, babura guda biyu, bindiga ƙirar PKT, da kuma rediyon sadarwa.
Bayan wannan lamari, dakarun soji sun ci gaba da gudanar da sintiri da kuma bin sahun maharan a yankunan da ke maƙwabtaka da sansanin domin kakkabe ragowar ’yan ta’adda.
Wannan nasara na ɗaya daga cikin ƙoƙarin da dakarun haɗin gwiwa ke yi na tabbatar da tsaro da kuma daƙile dukkanin wani yunƙurin na tada zaune-tsaye a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link