An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
[ad_1]
An gudanar da taron hadin kai na raya albarkatun kasa tsakanin lardin Shandong na kasar Sin da kasar Mozambique, a ranar Alhamis 9 ga watan nan a birnin Maputo, fadar mulkin kasar Mozambique, taron da ya zama wani muhimmin dandali na kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin sassan biyu.
A cikin jawabinsa yayin taron, mataimakin gwamnan lardin Shandong Wen Nuan ya ce, a nahiyar Afirka, kasar Mozambique muhimmiyar abokiyar huldar ce ta lardin Shandong. A shekarar 2024, darajar kasuwanci tsakanin Shandong da Mozambique ta kai dala miliyan 768, wanda ya karu da kashi 15.4 cikin dari, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Kazalika, a rabin farko na wannan shekara ta 2025, darajar kasuwanci tsakaninsu ta kai dala miliyan 420, adadin da ya nuna karuwar kashi 25.4 cikin dari.
Ya ce kamfanoni da dama na lardin Shandong sun zuba jari a Mozambique, kuma bangarorin biyu sun kara hadin gwiwa a fannonin noma, da hakar ma’adinai, da samar da ababen more rayuwa, matakin dake bayyana dankon zumunci dake tsakanin sassan biyu.
A nasa tsokaci kuwa, sakataren gwamnatin Mozambique mai kula da ma’adinai Jorge Daudo, cewa ya yi lardin Shandong yana daya daga cikin larduna masu kwazo da ci gaban masana’antu a Sin, kuma yana da karfi a fannonin hakar ma’adinai, da sarrafa karafa da masana’antu. Sabo da haka, Mozambique na fatan kara yin hadin gwiwa da lardin na Shandong. (Amina Xu)
[ad_2]
Source link