Sojoji Sun Kashe Ɗan Fashi, Sun Kama Ɓarayin Shanu A Binuwe Da Nasarawa
[ad_1]
Dakarun Operation Whirl Stroke (OPWS) sun ƙara zafafa ayyukan tsaro bisa sahihin bayanan sirri a jihohin Biniwe da Nasarawa, inda suka kashe wani ɗan fashi ɗauke da makami tare da kama wasu da ake zargi da fashi da satar shanu.
A cewar wata sanarwa da Laftanar Ahmad Zubairu Zubairu, muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na OPWS ya sanyawa hannu, ayyukan da aka gudanar tsakanin 3 zuwa 5 ga Fabrairu, 2026, sun haɗa da sintirin haɗin gwuiwa tsakanin sojoji, da ƴansanda da rundunar kare fararen hula ta Jihar Binuwe domin daƙile barazanar tsaro a yankunan karkara.
- Sin Ta Yi Imanin Karin Kamfanonin Mabambantan Kasashe Za Su Zo Hong Kong Don Zuba Jari Da Fara Kasuwanci
- Amurka Ta Tura Sojojinta Zuwa Nijeriya Don Taimakawa Yaƙi Da ’Yan Ta’adda
A ranar 3 ga Fabrairu, dakarun sashi na 1 na OPWS sun yi artabu da makiyaya ɗauke da makamai a ƙauyen Ayamba da ke ƙaramar Hukumar Katsina-Ala ta Jihar Benue, inda aka kashe ɗan fashi guda ɗaya, tare da kwato bindigar AK-47, mujallu biyu da harsashi uku.
Haka kuma a Nasarawa, dakarun sashi na 2 da ke sansanin Agyaragu sun kama wani da ake zargi da fashi, Adam Paul mai shekaru 34, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan da ake zargi da aikatawa a yankin Obi. A Binuwe kuma, dakarun bataliya ta musamman sun kama wasu mutane da ake zargi da satar shanu a Agagbe, tare da miƙa su ga ’yansanda domin bincike.
Kwamandan rundunar, Manjo Janar Moses Gara, ya yaba wa dakarun bisa jajircewa da ƙwazo, yana mai kira da a ci gaba da zafafa sintiri domin hana masu laifi samun damar aiwatar da ayyukansu. Ya kuma gode wa al’umma da sauran hukumomin tsaro kan goyon bayan da suke bayarwa.
[ad_2]
Source link