Da Ɗumi-Ɗumi: ‘Yan Jaridan Bauchi Sun Yi Hatsari Yayin Ɗaukan Rahoton Ayyukan NEDC
[ad_1]
Tawagar ‘yan jarida daga kafafen daban-daban sun gamu da mummunar hatsarin mota a yayin da suke cikin tawagar hukumar NEDC a ƙarƙashin jagorancin ƙaramin ministan raya yankuna, Alhaji Uba Maigari Ahmadu a yayin da suke zagayen buɗewa da miƙa ayyukan da hukumar NEDC ta gudanar a jihar Bauchi zuwa hannun gwamnatin jihar.
Hatsarin ya faru ne a kan titin Yashi zuwa Yelwan Duguri da ke cikin ƙaramar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi ranar Juma’a.
- Ɗan Majalisar NNPP Ɗaya Tilo A Bauchi Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC
- Gwamna Abba Kabir Ya Mayar Wa Da Bappa Bichi Martani
A halin da ake ciki wasu daga cikin ‘yan jaridan sun gamu da raunuka daban-daban yayin da ake ƙoƙarin samar musu da agajin gaggawa a asibitin Yelwan Duguri daga bisani kuma za a wuce da su babban asibiti a Bauchi domin neman musu kulawar likitoci.
‘Yan jaridan waɗanda suka fito daga gidajen talabijin na Channels, AIT, NTA, Arise da wasu mambobin Correspondents’ chapel irin su wakilan manyan jaridun da dama.
Hatsarin ya faru ne jimkaɗan bayan da tawagar suka buɗe aikin makarantar GSS a Yelwan Duguri inda suke kan hanyarsu ta zuwa domin buɗe wasu ayyukan.
Daga cikin waɗanda suke cikin tawagar har da minista, shugabannin NEDC, chairman da MD, mataimakin gwamnan jihar Bauchi da sauransu.
Kazalika, Wakilinmu wanda ke cikin tawagar ya shaida mana cewa motar da ta gamu da hatsarin ɗaya ce daga cikin motocin da ‘yan jaridan ke amfani da su a yayin aikin ɗauko labarin. Ya kuma tabbatar mana da cewa kayayyakin aikin jarida dama kamar su Kamarori sun lalace.
[ad_2]
Source link