Kungiyar SSANU Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Mutunta Yarjejeniyarsu Ta 2009

[ad_1]

Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Nijeriya (SSANU), ta bayar da wa’adin wata daya ga gwamnatin tarayya, da ta kammala tattaunawa kan yarjejeniyar 2009, ko kuma ta fuskanci yajin aiki na din-din-din.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, bayan taron majalisar zartarwa ta kasa karo na 54 da ta gudanar a jami’ar Jihar Ekiti.

  • Fadar Shugaban Ƙasa Ta Soki Jami’iyyar ADC, Ta Ce Su Fuskanci Matsalolinsu
  • Mutane Da Dama Sun Jikkata A Rikicin ‘Yan Daba A Kano

Sanarwar ta samu sa hannun shugaban SSANU na kasa, Muhammad Ibrahim.

Ibrahim ya yi gargadin cewa, rashin kammala tattaunawar nan na ranar 30 ga Afrilun 2026, zai sa kungiyar ba ta da wani zabi, illa shiga fara yajin aiki tare da hadin gwiwar kwamitin NASU da SSANU.

Ya soki yadda tattaunawar ke yin tafiyar hawainiya, yana mai nuni da rashin cika alkawari daga gwamnati.

Ya kuma yi Allah-wadai da jinkirin biyan albashi da kuma rashin karin albashi, yana mai cewa; lamarin ya kara tsananta ga mambobin kungiyar.

Kazalika, kungiyar ta kuma yi kira da a gaggauta daidaita albashin da ba a biya ba tare da daukar tsarin biyan kudi na bai-daya.

SSANU ta kuma yi zargin cewa, an cire wasu ma’aikata daga kudaden alawus-alawus na naira biliyan 50 da aka amince da su a shekarar 2022, inda suka dage cewa; a hada duk ma’aikatan da suka cancanta ba tare da nuna bambanci ba.

Kungiyar ta kuma nuna damuwa kan hauhawar farashin kayayyaki, karancin kudade na jami’o’i, rashin ingantaccen ababen more rayuwa da kuma rashin tsaro a harabar jami’o’in.

Kazalika, ya yi gargadin cewa; karancin kayan aikin kimiyya da fasaha da rashin isassun kudade na bincike, na iya lalata gasa ta ilimi a Nijeriya.

SSANU ta yi watsi da tsarin hadin gwiwar jama’a da masu zaman kansu wanda zai iya haifar da asarar ayyukan yi tare da yin kira da a ci gaba da tattaunawa, domin hana ci gaba da takaddamar jami’o’i.

Yanzu haka ‘yan Nijeriya za su iya saka hannun jari na kimanin naira miliyan 2.5 a kan manyan kamfanoni da kuma samun ribar kusan naira miliyan 17 zuwa naira miliyan 25. An biya duk abin da aka samu da dalar Amurka.

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *