Gwamnatin Oyo za ta sayi kwamfutoci 60,000 domin dalibai masu rubuta WAEC
[ad_1]
Gwamnatin Jihar Oyo ta ce za ta sayi na’urar kamfuta samfurin Laptop guda 60,000 domin gudanar da jarabawar kammala sakandare ta WAEC ta hanyar amfani da kwamfuta (CBT)
Wannan mataki ya yi daidai da umarnin Gwamnatin Tarayya na sauya tsarin jarabawa daga rubutu da takarda zuwa cikakken tsarin amfani da kwamfuta sannu a hankali.
A cewar sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Dotun Oyelade, ya fitar a ranar Juma’a, Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na jihar, Olusegun Olayiwola, ya bayyana hakan yayin ziyarar ban girma da Shugaban Shiyya kuma Mataimakin Magatakarda na WAEC, Waheed Amode, da tawagarsa suka kai ofishinsa.
“Gwamna Seyi Makinde ya bayar da umarnin a yi lissafin kuɗin da ake buƙata domin sayen kwamfutoci (Laptop) sama da 60,000 ga makarantun sakandare na gwamnati a fadin jihar,” in ji Olayiwola, yana mai cewa wannan mataki zai sanya Jihar Oyo gaba wajen cikakken karɓar tsarin CBT.
Ya yaba wa WAEC bisa matakan da ta ɗauka wajen magance ƙalubalen da aka fuskanta a jarabawar 2025, tare da alkawarin cewa ma’aikatarsa za ta ci gaba da tallafawa wajen hana maguɗin jarabawa da kuma kare kayan makarantu daga lalacewa.
A nasa jawabin, Amode ya ce sun kai ziyarar ce domin gode wa Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Oyo bisa goyon bayan da ta bayar a jarabawar WAEC ta 2025 da kuma haɗin gwiwar da ta ci gaba da yi da hukumar tsawon shekaru, yana mai bayyana ma’aikatar a matsayin babbar abokiyar hulɗa wajen nasarar ayyukan hukumar.
Ya kuma ce an rufe rajistar jarabawar WAEC ta watan Mayu/Yuni 2026 tun a ranar 2 ga watan Fabrairun 2026, yana mai cewa jarabawar da ke tafe za a gudanar da ita ta amfani da tsarin CBT da kuma rubutu da takarda, gwargwadon shirin kowace makaranta.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link