Sin Tana Tare Da Kungiyar G77

[ad_1]

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau 16 ga wannan wata cewa, a matsayin kasa mai tasowa mafi girma a duniya, kasar Sin ta kiyaye kasancewa tare da kasashe masu tasowa na duniya, da tsayawa tare da kungiyar G77, da tabbatar da adalci a duniya da kuma moriyar kasashe masu tasowa baki daya.

A kwanakin baya, an gudanar da bikin sauya shugabancin tsarin hadin gwiwar kungiyar G77 da kasar Sin a cibiyar MDD, inda kasar Uruguay ta zama sabuwar shugabar tsarin ta shekarar 2026.

Game da wannan batu, Guo Jiakun ya bayyana cewa, Sin tana taya kasar Uruguay murnar zama sabuwar shugabar tsarin a wannan karo. Kuma tsarin hadin gwiwar kungiyar G77 da kasar Sin muhimmin dandali ne na tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa da kyautata tsarin sarrafa harkokin duniya, kana ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ra’ayoyin bangarori daban daban, da kuma sauran harkokin kasa da kasa baki daya. (Zainab Zhang)

[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *