An kama wani mutum bisa zargin kashe matarsa da fartanya a Kebbi

[ad_1]



Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, ta kama wani mutum mai suna Suleman Mamuda, mai shekaru 30 a duniya bisa zargin kashe matarsa, Umaima Maidawa, a ƙauyen Bayawa da ke Ƙaramar Hukumar Augie.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya yi amfani da fartanya wajen dukan matarsa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarta.

Kakakin rundunar, SP Bashir Usman, ya ce bayan faruwar lamarin mutumin ya tsere, amma daga baya ’yan sanda suka gano inda ya ɓuya biyo bayan wasu bayanan da suka samu.

Ya ƙara da cewa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Umar Mohammed Hadejia, ya bayar da umarnin a miƙa lamarin zuwa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin ci gaba da bincike.

Hakazalika, ya ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.


[ad_2]

Source link

Similar Posts

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *