An kashe wani mutum a rikicin manoma da makiyaya a Yobe
[ad_1]
An kashe wani manomi mai suna Moh’d Abdullahi mai shekaru 50, a garin Mallam da ke Ƙaramar Hukumar Karasuwa a Jihar Yobe, bayan rikici ya ɓarke tsakaninsa da makiyaya a gonarsa.
Rahotanni sun ce wasu makiyaya uku; Usmanu Alh. Musa, Buba Alh. Manu da Ahmadu Inusa ne suka shiga gonarsa a ranar Laraba.
Lokacin da manomin ya hana su, sai suka harbe shi da kibiya, wanda ya ji mummunan rauni.
Bayan haka, wasu mazauna ƙauyen sun kai wa Ahmadu Inusa hari domin ramuwar gayya, inda shi ma ya jikkata.
An kai su asibiti a Gashuwa, inda likitoci suka tabbatar da rasuwar Abdullahi, yayin da Inusa ke karɓar magani.
An miƙa gawar marigayin ga iyalansa domin birne shi bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da ake ci gaba da bincike a kan lamarin.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Dungus Abdulkareem, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce rikici ne kan gona ya haddasa harbin, kuma ’yan sanda sun fara bincike tare da kama waɗanda abin ya shafa.
Ya ƙara da cewa da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.
Rundunar ta kuma yi kira ga manoma da makiyaya su zauna lafiya da juna, su guji shiga gonakin juna ko hanyoyin kiwo domin kaucewa irin wannan rikici.
Masu alaƙa
[ad_2]
Source link